Hausa Bible
Luka 21
1 Yesu ya ɗaga kai ya ga waɗansu masu kuɗi suna sa baikonsu a wurin zuba baiko.
2 Sai ya ga wata matalauciyar da mijinta ya mutu ta zo ta sa baiko na ˈyan tagulla biyun da ba su kai kobo ba.
3 Sai Yesu ya ce, “Hakika ina gaya muku, baikon da matalauciyar nan ta sa, ya fi na sauran duka.
4 Gama dukansu sun bayar daga yawan abin da suke da shi ne, amma ita kuwa cikin rashinta ta sa duk ɗan kuɗin da take da shi a rayuwarta.”
5 Waɗansu suka fara magana a kan Haikali, da adon duwatsu masu darajar da aka gina shi da su, da kuma irin kyautan da aka yi masa ado da su. Sai Yesu ya ce,
6 “Game da abubuwan nan da kuke kallo ne, to, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗanˈuwansa, kowannensu za a rushe shi.”
7 Sai suka tambaye shi suka ce, “Malam, yaushe wannan zai faru? Wace alama ce kuma za a gani saˈad da abubuwan nan za su faru?”
8 Sai ya ce musu, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku. Domin mutane da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi!’ da kuma, ‘Lokaci ya yi!’ Kada fa ku bi su.
9 Kada ma ku ji tsoro in kun ji labarin yaƙe-yaƙe da tashin hankali. Lallai ne wannan yă fara zuwa, amma ƙarshen bai zo ba tukuna.”
10 Ya ci gaba da cewa, “Alˈumma za ta tasar wa alˈumma, mulki yă tasar wa mulki.
11 Za a yi mummunar rawar ƙasa, da yunwa da balaˈi a wurare dabam-dabam. Za a ga abubuwa masu ban tsoro da alamu masu ban mamaki suna fitowa daga sama.
12 Kafin duk abubuwan nan su faru, za su kama ku, su ba da ku don a tsananta muku. Za a kai ku gaban majamiˈu a kuma sa ku a kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da shugabanni saboda sunana.
13 Wannan ne zai ba ku dama ku yi shaidar labarina.
14 Saboda haka sai ku shirya a ranku tun da wuri a kan ba za ku damu da yadda za ku kāre kanku ba.
15 Gama zan ba ku kalmomi da hikima yadda ko ɗaya daga cikin masu gāba da ku ba zai iya juye maganar ko yă yi musūn abin da kuka ce ba.
16 Har iyayenku ma, da ˈyanˈuwanku, da danginku, da abokanku za su bashe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku.
17 Kowa zai ƙi ku saboda sunana.
18 Amma ba ko ɗaya daga cikin gashin kanku da zai ɓata.
19 Idan kuka jimre, za ku tsira.
20 “Saˈad da kuka ga sojoji sun kewaye Urushalima, za ku sani cewa an yi kusa a rushe ta.
21 To, sai waɗanda suke cikin yankin Yahudiya, su gudu zuwa cikin tuddai. Waɗanda suke a birni kuma su fita, waɗanda suke a ƙauye kuma kada su shiga birnin.
22 Gama kwanakin nan kwanakin hukunci ne, don dole ne a cika duk abin da Rubutacciyar Maganar Allah ta ce.
23 Kaiton mata masu ciki da masu goyo a wannan lokaci! Gama mummunar wahala za ta shiga ƙasar, kuma fushin Allah zai sauko a kan mutanen nan.
24 Za a kashe waɗansu a yaƙi, a kuma kama waɗansu a kai su bauta a waɗansu ƙasashe. Waɗanda ba Yahudawa ba za su tsananta wa Urushalima, har sai lokacinsu ya cika.
25 “Za a kuma ga alamu masu ban tsoro a jikin rana, da wata, da taurari. A duniya kuma alˈummai za su rikice don tsoro saboda tafasa da haukan teku.
26 Mutane za su yi suma don tsoro, za su kuma razana da ganin abubuwan da suke faruwa ga duniya. Gama za a girgiza ikokin sararin sama.
27 Saˈan nan za a ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin girgije tare da iko da ɗaukaka mai yawa.
28 Idan waɗannan abubuwa suka fara faruwa, ku shirya kanku sosai domin cetonku ya yi kusa.”
29 Sai Yesu ya ba su wani misali ya ce, “Ku duba itacen ɓaure da sauran itatuwa mana.
30 Da zarar sun fara fitar da sababbin ganye, ku da kanku kun san cewa damina ta yi kusa ke nan.
31 Haka ma, idan kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.
32 “Hakika ina gaya muku mutanen zamanin nan ba za su mutu ba sai dukan abubuwan nan sun faru.
33 Sama da duniya za su shuɗe, amma kalmata ba za ta shuɗe ba ko kaɗan.
34 “Ku zauna a shirye fa. Kada ku bar ciye-ciye, da buguwa, da damuwar rayuwar duniya su ɗauki hankalinku. Idan ba haka ba, Ranar nan za ta zo ba labari ta cafke ku
35 kamar tarko. Gama za ta zo a kan kowa da yake zama a duniya duka.
36 Ku zauna a shirye fa, kuna adduˈa kullum don ku sami ƙarfin kuɓuce wa dukan waɗannan abubuwan da za su faru, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”
37 Kowace rana, Yesu yakan yi koyarwa a Haikali, amma idan yamma ta yi sai yă fita yă je Tudun Itatuwan Zaitun yă kwana a can.
38 Da sassafe kuma dukan mutane sukan zo wurinsa a Haikali su ji shi.