Hausa Bible
Luka 16
1 Yesu ya ce wa almajiransa, “An taɓa yin wani mai arziki wanda ya ba wakilinsa kaya yă lura masa da su. Daga baya an kawo masa labarin yadda wakilin nan yana banza da kayan maigidansa.
2 Sai maigidan ya kira wakilin ya ce masa, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo mini lissafin aikin da kake yi, domin ba za ka ƙara zama wakilina ba.’
3 Sai wakilin ya ce a ransa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ga shi ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunya in fara bara.
4 Yawwa! Na san abin da zan yi, don idan an kore ni daga aikina, mutane su karɓe ni a gidajensu.’
5 “Sai ya kira dukan mutanen da maigidansa yake binsu bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake binka?’
6 Ya ce, ‘Garwar mai guda ɗari.’ “Wakilin ya ce, ‘Ga takardarka, maza, ka rubuta hamsin.’
7 Ya kuma ce wa wani, ‘Kai fa, nawa ne ake binka?’ Sai shi kuma ya ce, ‘Buhun alkama guda ɗari ne.’ “Wakilin ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi tamanin.’
8 “Sai maigidan ya yabi wakilin nan marar gaskiya saboda ya yi wayo. Gama ˈyan zamani sun iya bi da mutanen zamaninsu da wayo fiye da mutanen haske.”
9 Yesu ya ci gaba da cewa, “Ina dai gaya muku, ku yi amfani da dukiyarku domin ku sami wa kanku abokai. Ta haka in dukiyar ta ƙāre, za a karɓe ku a gidaje na har abada.
10 Wanda ya isa a amince da shi a ƙaramin abu, za a iya amince da shi a babban abu ma. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, zai iya zama marar gaskiya ma a babban abu.
11 Idan fa ba ku yi aminci da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai ba ku amanar dukiya ta gaskiya?
12 Idan kuma ba ku yi aminci da kayan wani ba, wa ma zai ba ku wanda yake naku?
13 “Ba bawan da zai iya bauta wa shugabanni biyu, ko dai yă ƙi ɗaya, yă so ɗaya, ko kuwa yă yi wa ɗayan aminci, yă rena ɗayan. Ba dama ku sa ranku ga bin Allah ku kuma sa ga kuɗi duk gaba ɗaya.”
14 Da yake Farisiyawa masu son kuɗi ne, da jin abin nan da Yesu ya faɗa, sai suka yi tsaki.
15 Amma Yesu ya ce musu, “Ku ne masu son nuna a gaban mutane cewa ku masu adalci ne. Amma Allah ya san zuciyarku. Abubuwan da mutane suke ba su girma, su ne Allah ba ya ma son gani.
16 “Koyarwar Musa da ta annabawa ne abin da mutane suka yi ta bi har zuwa lokacin Yohanna Mai Baftisma. Amma tun da aka yi waˈazin labari mai daɗi na mulkin Allah, kowa yana ƙoƙari sosai yă sami shiga.
17 Duk da haka zai fi sauƙi sama da ƙasa su shuɗe, da a ce ɗigo ɗaya daga Koyarwar Musa yă ɓace.
18 “Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata, ya yi zina ke nan, kuma duk wanda ya auri matar da ta bar mijinta, zina ne yake yi da ita kawai.
19 “An yi wani mai arziki wanda yakan sa riguna masu tsada mai kalar jar garura, yakan kuma ci abinci mai kyau kowace rana.
20 A ƙofar gidansa kuwa akwai wani matalauci mai suna Liˈazaru, wanda miki sun rufe jikinsa. Akan kawo shi a kwantar da shi a nan kullum.
21 Shi kuwa yakan so yă ci ko da sauran abincin da ya fāɗi daga kan tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma suna zuwa su lashe mikinsa.
22 “Ana nan sai talakan nan ya mutu, malaˈiku suka ɗauke shi, suka ba shi wurin zama mai daraja tare da Ibrahim. Mai arzikin nan ma ya mutu aka kuma binne shi.
23 Ya je can gidan wuta yana shan wuya, sai ya ɗaga kai ya ga Ibrahim daga nesa, tare da Liˈazaru.
24 Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Liˈazaru ya sa ˈyar yatsarsa a ruwa yă ɗiga a harshena domin in ji ɗan sanyi, domin ina jin jiki a cikin wannan wuta!’
25 “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake a duniya, kana da abubuwa masu kyau, Liˈazaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu yana jin daɗi, kai kuwa kana shan wahala.
26 Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da ku akwai wani ƙaton rami mai zurfi sosai da aka shirya domin kada waɗanda suke son ƙetarewa daga can zuwa wurinmu su iya, kada kuma wani yă ƙetare daga wurinmu zuwa can.’
27 “Sai mai arzikin nan ya ce, ‘To, baba, ina roƙonka, ka aike shi zuwa gidan babana,
28 gama ina da ˈyanˈuwa guda biyar maza, yă je yă yi musu magana, kada su ma su zo nan wurin azaba mai zafi.’
29 “Ibrahim ya ce, ‘Ai, ˈyanˈuwanka suna da Koyarwar Musa da littattafan annabawa, su ji abin da suke faɗa musu.’
30 “Mai arzikin ya amsa masa ya ce, ‘Aˈa, baba Ibrahim, in dai wani ya tashi daga kabari ya je wurinsu za su tuba.’
31 “Amma Ibrahim ya ce, ‘Idan ba su ji abin da Koyarwar Musa da littattafan annabawa suke cewa ba, kai, ko da wani ya tashi daga kabari, ba za su ji shi ba!’ ”