Hausa Bible
Luka 14
1 Wata Ranar Hutu ta Mako, sai Yesu ya shiga gidan wani shugaban Farisiyawa domin yă ci abinci. Mutane kuwa suna zuba masa ido.
2 Sai ga wani da ƙafafunsa da hannuwansa sun kukkumbura ya zo wurin Yesu.
3 Sai Yesu ya tambayi malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa ya ce, “Dokarmu ta yarda a yi warkewa a Ranar Hutu, ko babu?”
4 Amma ba su ce kome ba. Yesu kuwa ya ɗauki mutumin ya warkar da shi, ya kuma ce masa yă tafi abinsa.
5 Saˈan nan Yesu ya tambayi mutanen, ya ce, “Idan jakinku ko bijiminku ya fāɗi a rijiya a Ranar Hutu ta Mako, ba za ku cire shi nan da nan ba wai don Ranar Hutu ne?”
6 Suka rasa amsar wannan tambaya.
7 Da Yesu ya ga waɗansu a cikin mutanen da aka gayyata don cin abinci suna ƙoƙarin zaɓar kujeru masu daraja, sai Yesu ya faɗa musu wannan misali.
8 “Idan wani ya kira ka zuwa bikin aure, kada ka je ka fara zauna a wurin zaman manya, gama wataƙila an kira wani wanda ya fi ka daraja.
9 Shi wanda ya kira ku duka biyu kuwa zai zo yă ce maka, ‘Tashi, ka ba wannan wuri.’ Ka ga, za ka ji kunya, don za ka koma kan wurin zama marar daraja.
10 Amma idan an kira ka biki, ka je ka nemi wurin zama marar daraja ka zauna, don in wanda ya kira ka ya zo, sai yă ce maka, ‘Zo nan, abokina, ka zauna a wannan kujera mai daraja.’ Wannan zai sa sauran mutanen da aka kira, su ba ka girma.
11 Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, amma duk wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
12 Sai Yesu ya ce wa wanda ya kira shi, “Idan ka kira wani don cin abinci, ko ka shirya biki, kada ka kira abokanka ne kawai, ko ˈyanˈuwanka, ko danginka, ko maƙwabtanka masu arziki, don wata rana za su kira ka, su ma. Ta haka za su biya ka abin da ka yi musu.
13 Amma in za ka kira mutane biki, ka kira talakawa, da guragu, da shanyayyu da makafi.
14 Ta haka za ka sami albarka, domin waɗannan dai ba za su iya biyanka ba. Allah ne zai biya ka a ranar da masu adalci za su tashi daga matattu.”
15 Da jin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da shi a tebur ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne duk wanda zai ci abinci a bikin nan na mulkin Allah!”
16 Yesu ya ce masa, “An taɓa yin wani mutumin da ya shirya babban biki, ya kuma kira mutane da yawa.
17 Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa yă je yă ce wa waɗanda aka kira, ‘Ku zo, gama an gama shirya kome!’
18 Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farko ya ce, ‘Na sayi gona, dole ne in je in gani yadda take, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’
19 Ɗayan kuma ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma, ina hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’
20 Wani kuma ya ce, ‘Kwana-kwanan nan ne na yi aure, saboda haka ba zan sami damar zuwa ba.’
21 “Bawan ya koma ya gaya wa maigidansa dukan abin da aka gaya masa. Haushi ya kama maigidan, sai ya ce wa bawan, ‘Yi maza, ka bi titi-titi da lungu-lungu na birni, ka tattara talakawa, da guragu, da makafi, da shanyayyu ka kawo su nan.’
22 Nan da nan, bawan ya dawo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, an yi abin da ka faɗa, amma da sauran wuri har yanzu.’
23 Maigidan ya ce wa bawan, ‘Ka je kan manyan hanyoyi da ƙanana, ka turo mutane su zo, don gidana yă cika.
24 Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da dā aka kira da zai ɗanɗana abincin bikin nan da na shirya.’ ”
25 Wata rana, mutane da yawa suna bin Yesu, sai ya juya ya ce musu,
26 “Duk mai son bina, in bai fi ƙaunata fiye da babansa, ko mamarsa, ko matarsa, ko ˈyaˈyansa, ko ˈyanˈuwansa maza da mata, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.
27 Duk wanda bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.
28 “Misali, idan wani daga cikinku yana so yă yi gini, zai fara zauna, yă yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna yă gani ko yana da isasshen kuɗin da zai gama ginin.
29 In bai yi haka ba, ba zai iya gama ginin da ya fara ba, kuma dukan mutanen da suka ga wannan aiki za su yi masa dariya,
30 za su ce, ‘Wannan mutum ya fara gini amma ya kāsa gamawa.’
31 “Idan wani sarki zai fita da sojoji dubu goma domin yă yi yaƙi da wani wanda yake da sojoji dubu ashirin, ai, zai zauna tukuna yă duba ko yana da isasshen ƙarfin da zai yaƙi wancan sarkin.
32 Idan ba zai iya ba, to, tun suna da nisa sai yă aika da ˈyan aika su je su nemi hanyar zaman lafiya.
33 Haka ma kowannenku in bai bar duk abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.”
34 “Gishiri abu ne mai kyau, amma idan ya rabu da daɗinsa, ta yaya za a mai da daɗinsa?
35 Ba shi da wani amfani a gona, ko a taki, sai dai a zubar da shi kawai. Bari mai kunnen ji, yă ji.”