Hausa Bible
Yahaya 7
1 Bayan wannan Yesu ya zazzaga cikin Galili, amma bai so yă yi tafiya cikin Yahudiya ba, don Yahudawan da suke can suna nema su kashe shi.
2 Bikin Bukkoki na Yahudawa ya yi kusa ke nan,
3 sai ˈyanˈuwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka tashi daga nan ka tafi Yahudiya domin almajiranka su ma su ga ayyukan ban mamakin da kake yi.
4 Ai, duk wanda yake so a san shi sosai ba ya ɓoye abin da yake yi. Tun da yake kana yin waɗannan abubuwa, ai, sai ka nuna kanka domin duniya ta san ka.”
5 Gama su ˈyanˈuwan Yesu ma ba su ba da gaskiya gare shi ba.
6 Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai zo ba tukuna, amma a wajenku kowane lokaci daidai ne.
7 Ku kam duniya ba za ta iya ƙinku ba, amma ni take ƙi, domin ina faɗa mata mugayen ayyukan da take yi.
8 Ku dai ku tafi bikin. Ni ba zan tafi wannan biki ba, gama lokacina bai yi ba tukuna.”
9 Bayan da Yesu ya faɗa musu wannan magana, sai ya ɗan dakata a Galili.
10 Amma bayan da ˈyanˈuwansa suka tafi bikin, sai Yesu ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba.
11 Yahudawa suna ta nemansa a wurin bikin, suna tambaya cewa, “Ina mutumin yake?”
12 A cikin taron nan mutane suna ta maganganu da junansu a ɓoye a kan Yesu. Waɗansu suna cewa, “Shi mutumin kirki ne.” Waɗansu kuma suna cewa, “Aˈa, ai, yana ruɗin mutane ne.”
13 Amma ba wanda ya yi ƙarfin hali yă yi magana a kan Yesu a fili, saboda suna tsoron shugabannin Yahudawa.
14 Da aka ci rabin lokacin biki, sai Yesu ya shiga Haikali ya fara koyarwa.
15 Sai shugabannin Yahudawa suka yi mamaki suka ce, “Wannan mutum bai taɓa zuwa makaranta don koyon karatu ba, ta yaya ya zama gwani haka?”
16 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Abubuwan da nake koyarwa ba nawa ba ne, amma na wanda ya aiko ni ne.
17 Duk wanda ya zaɓi yin abin da Allah yake so, zai sani cewa koyarwata ta fito daga wurin Allah ne, ba wurina ba.
18 Wanda yake koyar da abubuwa na kansa, yana ƙoƙarin ɗaukaka kansa ne. Amma wanda yake ƙoƙarin ɗaukaka wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, kuma ba shi da rashin gaskiya a cikinsa.
19 Ashe, ba Musa ne ya ba ku Koyarwa ba? Amma duk da haka ba wani a cikinku wanda yake kiyaye Koyarwar. Me ya sa kuke so ku kashe ni?”
20 Mutanen suka amsa suka ce, “Kana da aljani a cikinka. Su wane ne suke so su kashe ka?”
21 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Na yi abin ban mamaki guda ɗaya tak, amma kun yi mamaki dukanku.
22 Musa ya ba ku umarnin kaciya, ko da yake ba shi ne ya fara ba, amma kakannin kakanninku ne. Duk da haka kukan yi wa yaro kaciya a Ranar Hutu ta Mako.
23 To, idan ana iya yi wa yaro kaciya a Ranar Hutu ta Mako domin dai a yi biyayya da Koyarwar Musa, to, me ya sa za ku yi fushi da ni saboda na warkar da jikin mutum sarai a Ranar Hutu?
24 Kada ku yi shariˈa bisa ga yadda abubuwa suke a ganin ido, amma ku yi shariˈa bisa ga abin da yake daidai.”
25 Sai waɗansu mutanen Urushalima suka ce, “Ashe, ba wannan ne mutumin da suke nema su kashe ba?
26 Ga shi nan kuwa, yana magana a fili, ba su ce masa kome ba. Ko shugabannin sun riga sun yarda cewa shi ne Almasihu ke nan?
27 Ga shi, mun san inda mutumin nan ya fito, amma saˈad da Almasihu na gaske ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.”
28 Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san inda na fito. Amma ban zo da ikon kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba.
29 Amma ni na san shi, gama daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.”
30 Da Yesu ya faɗa wannan magana, sai mutanen suka nema su kama shi. Amma ba wanda ya taɓa shi, gama lokacinsa bai yi ba.
31 Duk da haka mutane da yawa a cikin jamaˈar suka gaskata da Yesu, suna cewa, “Shin, lokacin da Almasihu zai zo, zai yi alamun ban mamaki fiye da abubuwan da mutumin nan ya yi ne?”
32 Farisiyawa suka ji mutane suna magana a hankali da juna a kan Yesu, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin Haikali su kamo shi.
33 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Lokacin da zan zauna tare da ku ya rage ɗan kaɗan, saˈan nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.
34 Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba. Inda nake kuwa ba za ku iya zuwa ba.”
35 Sai Yahudawa suka yi magana da juna suka ce, “Ina ne zai tafi har da ba za mu same shi ba? Ko za shi wajen Yahudawan da suke a warwatse suna zama da Helenawa ne, yă koya wa Helenawa a can?
36 Me yake nufi da ya ce, ‘Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba’? Me yake nufi kuma da ‘Inda nake ba za ku iya zuwa ba’?”
37 A ranar ƙarshe ta bikin, wadda kuma ta zama babbar rana ta bikin, Yesu ya tsaya ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishin ruwa yă zo wurina yă sha.
38 Duk mai ba da gaskiya gare ni, ‘Rafuffukan ruwa mai ba da rai za su fiffito daga zuciyarsa,’ kamar yadda Rubutacciyar Maganar Allah ta faɗa.”
39 Yesu yana magana ne a kan Ruhu Mai Tsarki, wanda masu ba da gaskiya gare shi za su karɓa, domin a wannan lokaci ba a ba da Ruhu Mai Tsarki ba tukuna, saboda ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
40 Da mutanen suka ji wannan maganar da Yesu ya yi, sai suka ce, “Ba shakka, wannan shi ne Annabin nan.”
41 Waɗansu kuwa suka ce, “Wannan shi ne Almasihun.” Amma har yanzu waɗansu suka ce, “Ashe, Almasihun daga Galili zai fito?
42 Ba Rubutacciyar Maganar Allah ta faɗa cewa Almasihu zai fito daga zuriyar Dawuda ne ba? Ba kuma zai fito daga Betelehem, ƙauyen da Dawuda ya zauna ne ba?”
43 Sai bakin mutanen ya rabu a kan Yesu.
44 Waɗansunsu suka so su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi.
45 Da masu gadi suka koma, sai manyan firistoci da shugabannin Farisiyawa suka tambaye su suka ce, “Me ya sa ba ku kawo shi ba?”
46 Sai dogarawan suka amsa suka ce, “Ai, babu mutumin da ya taɓa magana kamar wannan mutum.”
47 Farisiyawan suka ce wa dogarawan, “Af! Har ku ma ya ruɗe ku ke nan?
48 Ko akwai wani daga cikin shugabanni ko Farisiyawan da ya ba da gaskiya gare shi?
49 Amma wannan taron da ba su san kome a kan Koyarwar Musa ba, ai, laˈanannu ne.”
50 Nikodimus kuwa wanda ya je wurin Yesu a dā, wanda kuwa yana ɗaya daga cikin ƙungiyarsu, ya ce musu,
51 “Bisa ga Koyarwarmu ba za mu iya hukunta mutum ba, sai an ji daga bakinsa, don a san abin da yake yi.”
52 Sai suka amsa masa suka ce, “Kai ma mutumin Galili ne? Ka bincika Rubutacciyar Maganar Allah ka gani mana, ai, ba wani annabin da zai zo daga Galili.” [
53 Sai kowa ya tafi gida.