Hausa Bible
Ibraniyawa 8
1 Manufar maganarmu duka ita ce muna da Babban Firist wanda yake zaune a hannun daman kujerar mulkin Maɗaukaki a can sama.
2 Wannan Babban Firist kuwa yana hidimarsa a Wuri Mai Tsarki, a ainihin tentin kasancewar Allah wanda Ubangiji da kansa ne ya kafa, ba mutum ba.
3 Akan naɗa kowane babban firist ne domin yă miƙa baye-baye da hadayu. Haka kuma ya zama dole ne Babban Firist nan namu yă kasance da abin da zai miƙa.
4 Da a ce yana nan a duniya ne, da bai zama firist ba ko kaɗan, domin dā ma akwai firistoci waɗanda sukan miƙa baye-baye bisa ga Koyarwar Musa.
5 Firistocin nan kuwa sukan yi hidimarsu a cikin Wuri Mai Tsarki wanda yake kamanni da kwatanci na abubuwan da suke a sama. Gama a lokacin da Musa zai kafa Tentin Kasancewar Allah, an yi masa gargaɗi cewa, “Ka tabbata ka shirya kome da kome bisa ga kwatancin da aka nuna maka a kan babban tudun.”
6 Amma yanzu an ba Yesu aikin firist wanda yake mafi kyau, kamar yadda yarjejeniyar nan take mafi kyau, wadda Yesu shi ne mai tsayawa tsakanin Allah da mutane. Yarjejeniyar nan kuwa mafi kyau ce gama an kafa ta a kan alkawaran da sun fi kyau.
7 Da a ce yarjejeniya ta farko ba ta da kāsawa, ai, da ba dalili a nemi wata mai biye da ita.
8 Amma Allah ya ga laifin mutanensa saˈad da ya ce, “Lokaci yana zuwa, in ji Ubangiji, da zan shirya sabuwar yarjejeniya da jamaˈar Israˈila tare da jamaˈar Yahuda.
9 Wannan ba za ta zama kamar yarjejeniya wadda na yi da kakanninsu ba, a ranar da na kama su a hannu na bi da su daga ƙasar Masar, gama ba su yi aminci da yarjejeniyata ba, sai na ƙyale su, in ji Ubangiji.
10 Ga yarjejeniyar da zan yi da jamaˈar Israˈila bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa koyarwata a cikin hankalinsu, zan kuma rubuta su a allon zuciyarsu. Zan zama Allahnsu, su kuwa su zama jamaˈata.
11 Ba za su bukaci su koya wa juna ba, ko kuwa wani yă ce wa ɗanˈuwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ gama dukansu za su san ni, daga mafi ƙanƙantansu zuwa mafi girma.
12 Gama zan yafe laifofinsu, ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”
13 Da Allah ya yi magana haka game da sabuwar yarjejeniya, ya mai da ta farkon tsoho ke nan. Kuma kowane abin da yake iri na dā, da yake tsufa kuma, zai shuɗe ba da daɗewa ba.