Hausa Bible
Ibraniyawa 3
1 Saboda haka, ˈyanˈuwana tsarkaka, ku da kuka sami kiran nan na sama ku ma, ku yi tunani a kan Yesu wanda shi ne Manzo da Babban Firist na bangaskiyar da muke shaida.
2 Yesu ya yi aminci ga wanda ya zaɓe shi, kamar yadda Musa ya yi aminci a aikinsa a cikin jamaˈar Allah.
3 Mutumin da ya gina gida ya fi gidan daraja. Haka kuma Yesu ya isa a ɗaukaka shi fiye da Musa.
4 Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma Allah ne ya gina kome.
5 Musa ya yi aminci a aikinsa na bawa a cikin jamaˈar Allah, ya kuma yi shaida game da abubuwan da za a faɗa nan gaba.
6 Amma Almasihu ya yi aminci a kan shi Ɗa ne wanda an ba shi iko a kan dukan jamaˈar Allah. Mu ne kuma jamaˈar nan tasa idan mun ci gaba da ƙarfin zuciyarmu, muna kuma sa zuciya ga abubuwan da muke bege a kansu.
7 Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau idan kun ji muryar Allah,
8 kada ku yi taurin zuciya kamar yadda kuka yi a lokacin tawayen nan, kamar ranar da aka gwada ni a daji.
9 A can ne kakanninku suka gwada ni, suka ga ayyukana har shekara arbaˈin.
10 Shi ya sa na yi fushi da wancan tsara, sai na ce, ‘Kullum suna ƙina a zuciyarsu, ba su kuwa san hanyoyina ba.’
11 Sai na yi fushi na yi rantsuwa cewa, ‘Ba za su shiga hutuna ba sam.’ ”
12 ˈYanˈuwana, ku tabbata cewa ba wani a cikinku wanda zunubi da rashin bangaskiya a zuciyarsa sun sa shi yă juya baya ga Allah Mai Rai.
13 Amma ku dinga ƙarfafa juna kowace rana. Ku yi amfani da kowane zarafi wanda ake ce da shi “Yau”, domin kada ko ɗayanku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗu na zunubi.
14 Mu masu tarayya da Almasihu ne idan mun tsaya da ƙarfi a kan amincewarmu ta fari har zuwa ƙarshe.
15 Kamar yadda aka ce, “Yau idan kun ji muryar Allah, kada ku yi taurin zuciya kamar yadda kuka yi a lokacin tawayen nan.”
16 Su wane ne waɗanda suka ji muryar Allah, duk da haka, suka yi masa tawaye? Ai, su ne dukan mutanen da Musa ya bi da su daga ƙasar Masar.
17 Su wane ne waɗanda Allah ya yi fushi da su har shekara arbaˈin? Ai, su ne waɗanda suka yi zunubi, suka fāɗi suka mutu a daji.
18 Su wane ne waɗanda Allah ya yi rantsuwa a kansu cewa ba za su shiga hutunsa ba sam? Ai, su ne waɗanda suka ƙi yin biyayya.
19 Saboda haka mun ga cewa rashin bangaskiya ne ya sa ba su iya shiga hutun nan ba.