Skip to content

Hausa Bible

Kolosiyawa 4

1 Ku iyayengiji, ku riƙe bayinku cikin gaskiya da adalci, gama kun sani cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama.

2 Ku nace cikin adduˈa, kuna tsaro a cikinta da godiya.

3 Ku kuma yi mana adduˈa, yadda Allah zai buɗe mana hanyar da za mu shaida kalmarsa, mu sanar wa mutane asirin nan na Almasihu. Saboda asirin nan ne nake a kurkuku.

4 Ku yi mini adduˈa in bayyana asirin nan sosai, kamar yadda ya kamata in yi.

5 A cikin zamanku tare da marasa bi, ku yi kome da hikima, kuna amfani da kowane zarafin da kuke da shi.

6 A koyaushe, bari maganarku ta kasance da alheri da kuma daɗin ji, domin ku san irin amsar da ya yi kyau ku ba kowa.

7 Tikikus zai gaya muku kome game da yadda nake a nan. Shi ɗanˈuwanmu ne wanda muke ƙauna sosai, kuma shi mai aminci ne cikin hidimar Ubangiji tare da mu.

8 Abin da ya sa na aike shi wurinku shi ne domin ku ku san labarin lafiyarmu, saˈan nan kuma yă ƙarfafa zuciyarku.

9 Ga kuma Onisimus tare da shi, ɗanˈuwanmu mai aminci wanda muke ƙauna, wanda shi ma ɗan wajenku ne. Su biyun za su faɗa muku dukan abin da yake faruwa a nan.

10 Aristarkus, wanda yake a kurkuku a nan tare da ni, ya ce in gaishe ku, haka kuma Markus wanda kakansa ɗaya ne da Barnaba. Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu.

11 Yoshuwa wanda ake ce da shi Yustus, shi ma yana gaishe ku. Waɗannan mutane uku su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi waɗanda suke yin aikin mulkin Allah tare da ni, sun kuma zama abin taˈaziyya a gare ni.

12 Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, wanda shi ma bawan Yesu Almasihu ne, yana gaishe ku. Kullum yana kokawa cikin adduˈa ga Allah domin ku tsaya daram, ku kuma zama cikakku, kuna da tabbaci a cikin dukan nufin Allah.

13 Ni kaina na shaida yadda shi Abafaras yake aiki da ƙwazo domin yă taimake ku, ku da kuma mutanen Lawudikiya da na Hirafolis.

14 Luka, likitan nan da muke ƙauna, da kuma Demas, suna gaishe ku.

15 Ku gai da dukan ˈyanˈuwan da suke Lawudikiya, da kuma Nimfa tare da jamaˈar masu bin Yesu da take taruwa a gidanta.

16 In an gama karanta wannan wasiƙa a gabanku, sai ku aika da ita zuwa ga jamaˈar masu bin Yesu da take a Lawudikiya, domin su ma su karanta. Ku ma ku karanta wasiƙar da mutanen Lawudikiya za su aika muku.

17 Ku kuma gaya wa Arkibus yă ba da hankali yă cika aikin nan da Ubangiji ya ba shi.

18 Ni Bulus ne da hannuna nake rubuta muku wannan gaisuwa. Kada ku manta ina cikin sarƙoƙi. Alherin Allah yă kasance tare da ku. Amin.

Open Bible reader