Hausa Bible
Ayyukan Manzanni 8
1 Shawulu kuwa ya goyi bayan kisan Istifanus. A ranar nan kuwa, wani babban tsanani ya fāɗa wa jamaˈar masu bin da take a Urushalima. Duk aka warwatsa ta a yankin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin ne kawai suka rage.
2 Sai waɗansu masu bauta wa Allah suka binne Istifanus, suka yi makoki sosai dominsa.
3 Amma Shawulu ya yi ta tsananta wa jamaˈar masu bi ƙwarai da gaske, yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata, yana sa su cikin kurkuku.
4 To, waɗanda aka warwatsar ɗin nan kuwa, suka yi ta zazzagawa suna yin shelar labarin nan mai daɗi.
5 Filibus ya tafi birnin Samariya, yana yi musu waˈazin Almasihu.
6 Da mutane suka ji, suka kuma ga alamun ban mamakin da yake yi, da nufi ɗaya suka mai da hankali ga abin da ya faɗa.
7 Ƙazaman ruhohi kuwa da ihu suka fito daga jikin mutane da yawa. Aka warkar da shanyayyu da guragu da yawa.
8 Saboda haka aka yi farin ciki sosai a birnin.
9 Akwai wani mutum kuwa mai suna Siman, wanda dā yake yin sihiri a birnin, har yana ba Samariyawa mamaki, yana cewa shi wani babban mutum ne.
10 Jamaˈa duka kuwa suka mai da hankali a kansa, babba da yaro, suna cewa, “Mutumin nan, ai, ikon nan na Allah ne, da ake ce da shi Mai Girma.”
11 Sai suka mai da hankali sosai a kansa, gama ya daɗe yana ta ba su mamaki da sihirinsa.
12 Amma da suka gaskata labari mai daɗin da Filibus ya yi a kan mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, dukansu aka yi musu baftisma, maza da mata.
13 Har Siman da kansa ma ya ba da gaskiya. Bayan an yi masa baftisma kuma ya manne wa Filibus. Da ya ga yadda Filibus yake yin alamu da manyan ayyukan ban mamaki, sai ya yi mamaki ƙwarai.
14 To, da manzannin da suke Urushalima suka ji Samariyawa sun karɓi kalmar Allah, sai suka aika musu Bitrus da Yohanna.
15 Su kuwa da suka iso, suka yi musu adduˈa su karɓi Ruhu Mai Tsarki.
16 Domin Ruhu Mai Tsarki bai sauko wa waninsu ba tukuna, sai dai kawai an yi musu baftisma ne da sunan Ubangiji Yesu.
17 Sai Bitrus da Yohanna suka sa musu hannun albarka, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.
18 To, da Siman ya ga, ashe ta sa hannun manzanni ne ake samun Ruhun, sai ya miƙa musu kuɗi,
19 ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iko, domin duk wanda na sa masa hannu, yă sami Ruhu Mai Tsarki.”
20 Amma Bitrus ya ce masa, “Kai da kuɗinka, ku halaka! Kana tsammani da kuɗi ne za ka sami kyautar Allah?
21 Ba ruwanka da wannan shaˈani ko kaɗan, gama zuciyarka ba daidai take ba a gaban Allah.
22 Sai ka tuba daga wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko zai gafarta maka abin nan da ka shirya a zuciyarka.
23 Gama na ga kana cike da mugun kishi, kana ɗaure cikin zunubi.”
24 Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku roƙe mini Ubangiji, kada ko ɗaya daga cikin abubuwan da kuka faɗa yă faru da ni.”
25 To, bayan da Bitrus da Yohanna suka yi shaida suka kuma yi waˈazin labari mai daɗi na maganar Ubangiji, sai suka koma Urushalima. Yayin da suke komawa Urushalima, sai suka yi ta yin waˈazin labari mai daɗi a ƙauyukan Samariya da yawa.
26 Ana nan sai wani malaˈikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Tashi ka bi ta kudu, ka bi hanyar da ta fito daga Urushalima zuwa Gaza,” wato hanyar hamada.
27 Sai ya tashi ya tafi. Sai ga wani mutumin Itiyofiya wanda shi bābā ne, wato an dandaƙe shi, mai babban matsayi a mulkin Kandis, sarauniyar Itiyofiya. Shi ne kuma maˈajin sarauniyar. Ya zo Urushalima ne domin yă yi sujada.
28 Da yana komawa gida a zaune cikin keken-dokinsa, ya buɗe littafin annabi Ishaya yana karatu.
29 Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa, ka yi kusa da keken-dokin nan.”
30 Sai Filibus ya gudu zuwa wurinsa, ya ji shi yana karatun littafin annabi Ishaya. Sai Filibus ya tambaye shi, “Ka gane abin da kake karantawa kuwa?”
31 Sai ya amsa, “Ina fa? Sai ko wani ya yi mini fassara.” Sai ya ce wa Filibus yă hau keken-dokin su zauna tare.
32 Ga sashen Rubutacciyar Maganar Allah da yake karantawa, “An kai shi kamar tunkiya zuwa wurin yanka. Kamar yadda ɗan rago yake shiru a hannun mai aski masa gashin jikinsa, haka bai ko buɗe bakinsa ba.
33 An yi masa wulaƙanci har an hana masa gaskiyarsa. Wa zai iya bayyana labarin zuriyarsa? Gama an ɗauki ransa daga duniya.”
34 Sai bābān nan ya ce wa Filibus, “A kan wane ne annabin nan yake magana? A kansa ne ko a kan wani?”
35 Sai Filibus ya buɗe bakinsa ya fara tun daga wannan sashen Rubutacciyar Maganar Allah, yana ba shi labari mai daɗi na Yesu.
36 Suna cikin tafiya ke nan, suka kai wurin ruwa, sai bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa! Mene ne zai hana a yi mini baftisma?”
37 Filibus ya ce, “Idan dai ka gaskata da zuciya ɗaya, ai, sai a yi maka.” Bābā nan ya ce, “Na gaskata, Yesu Almasihu Ɗan Allah ne.”
38 Sai ya ba da umarni a tsai da keken-dokin. Dukansu biyu suka sauka suka shiga cikin ruwan, sai Filibus ya yi wa mutumin nan baftisma.
39 Da suka fito daga cikin ruwan, Ruhun Ubangiji ya ɗauki Filibus, bābān bai sāke ganinsa ba. Sai mutumin ya yi tafiyarsa yana farin ciki.
40 Amma Filibus ya ga kansa a Azotus. Sai ya zazzaga dukan garuruwan, yana ba da labari mai daɗi, har ya kai Kaisariya.