Skip to content

Hausa Bible

Filibiyawa 3

1 A ƙarshe kuma, ˈyanˈuwa, ku yi farin ciki cikin Ubangiji. Bai dame ni in sāke rubuta muku waɗannan abubuwa ba. Ga shi kuwa, domin amfaninku ne.

2 Ku yi hankali da karnukan nan, masu mugayen ayyuka, masu yankan jikin nan, wai suna kaciya.

3 Ai, mu ne masu kaciya ta ainihi, mu da muke bauta wa Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki, masu taƙama da Almasihu Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan alˈadar mutum ba,

4 ko da yake ni ina iya dogara da ayyukan alˈadar mutum. Idan kuma akwai wanda yake tsammani yana da dalilin dogara da ayyukan alˈadar mutum, to, ni na fi shi.

5 Ga shi, an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina, ni ɗan Israˈila ne, na zuriyar Benyamin, cikakken ɗan Ibraniyawa kuwa. Game da bin Koyarwar Musa kuwa, ni Bafarisiye ne.

6 Game da ƙwazon bin addini kuma ina tsananta wa jamaˈar masu bin Yesu. Game da adalci ta wurin kiyaye dokokin Koyarwar Musa kuma, ba ni da laifi.

7 Amma abin da dā ya zama mini riba, yanzu na lissafta su hasara ce saboda Almasihu.

8 Ai, na mai da dukan abubuwa hasara, saboda darajar sanin Almasihu Yesu Ubangijina, darajar da ta fi kwatanci. Saboda Almasihu na zaɓi yin hasarar dukan abubuwa. Na mai da su abin banza, domin in sami riba ta zumunci da Almasihu,

9 in kuma zama a cikinsa. Wannan kuwa ba saboda adalcina ta wurin kiyaye Koyarwar Musa ba, sai dai ta wurin adalcin nan wanda yake fitowa daga bangaskiya cikin Almasihu, wato adalcin nan da ake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya.

10 Ina so in san Almasihu da ikon tashinsa daga matattu, da kuma tarayya cikin shan wuyarsa, in zama kamarsa cikin mutuwarsa.

11 Domin ko ta yaya in kai ga tashin nan daga matattu.

12 Ba wai na riga na zama yadda ya kamata in zama ba, ko kuma na riga na zama cikakke ba, aˈa, sai dai ina ta fama in yi nasara, domin Almasihu Yesu ya riga ya mai da ni nasa.

13 To, ˈyanˈuwa, ban ce na riga na kai ga nasarar nan ba, amma abu ɗaya nake yi, ina mantawa da abin da ya riga ya wuce, ina ƙoƙarin yin abin da yake gaba.

14 Ina nacewa gaba gaba in sami ladan nasara, wanda shi ne dalilin kiran nan zuwa sama, wanda Allah ya yi mini ta wurin Almasihu Yesu.

15 Saboda haka dukanmu da muka yi girma cikin ruhaniya, sai mu ɗauki wannan tunani. Amma idan waɗansunku suna da wani raˈayi dabam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma.

16 Babban abin shi ne duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.

17 ˈYanˈuwana, ina so ku bi gurbina, ku kuma dubi waɗanda tafiyarsu ta cancanta da yadda muka nuna muku.

18 Akwai waɗansu mutanen da na sha yi muku gargaɗi a kansu. Ina kuma sāke gaya muku yanzu, har da hawaye cewa tafiyarsu ta mai da su masu gāba da mutuwar Almasihu a kan gicciye.

19 Ƙarshensu halaka ne. Allahnsu cikinsu ne. Rashin kunyarsu shi ne abin taƙamarsu. Sun kafa ransu a kan alˈamuran duniya.

20 Mu dai ˈyan mulkin sama ne. Ai, muna jiran zuwan Mai Ceto, Ubangiji Yesu Almasihu, wanda zai zo daga can.

21 Shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai canja jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.

Open Bible reader