Hausa Bible
Filiman 1
1 Daga Bulus, ni da nake a kurkuku saboda Almasihu, da kuma ɗanˈuwanmu Timoti, zuwa ga Filimon abokin aikinmu wanda muke ƙauna,
2 da kuma ga Afiya ˈyarˈuwarmu da Arkibus ɗanˈuwanmu cikin fama, da kuma zuwa ga jamaˈar masu bin Yesu waɗanda suke taruwa a gidanka.
3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu su kasance tare da ku.
4 Nakan gode wa Allahna kullum saˈad da na tuna da kai a cikin adduˈata.
5 Gama ina jin labarin bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kake nuna wa dukan tsarkaka.
6 Ina adduˈa cewa za ka aikata alheri a yalwace, wanda ya fito daga bangaskiyarka, wannan ma zai kai ga zurfin ganewa game da dukan abubuwa masu kyau waɗanda suke namu cikin Almasihu.
7 Ɗanˈuwana, ƙaunarka ta kawo mini farin ciki ainun da kuma ƙarfafawa sosai saboda zukatan tsarkaka sun sami ƙarfafawa ta wurinka.
8 Saboda yadda kake ƙaunar masu bi, ina iya yin ƙarfin hali cikin Almasihu in umarce ka ka yi abin da ya kamata.
9 Amma saboda ina ƙaunarka, ni Bulus na fi so in roƙe ka, ni da nake tsoho yanzu kuma ina nan a cikin kurkuku saboda Almasihu Yesu.
10 Ina roƙonka a madadin ɗana Onisimus wanda na zama kamar baba a gare shi saˈad da nake a kurkuku.
11 A dā ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama mai amfani a gare ka da kuma a gare ni.
12 Ina aikarsa yanzu yă koma gare ka, shi wanda zuciyata duka take a kansa.
13 Yayin da nake a nan kurkuku saboda labari mai daɗi, na fi so in riƙe shi a wurina domin yă dinga yi mini hidima a madadinka.
14 Amma dai ba na so in yi wani abu ba tare da na sami yardarka ba, domin kada alherinka yă zama kamar na tilas ne, ba na yardar rai ba.
15 Wataƙila Onisimus ya rabu da kai na ɗan lokaci kaɗan ne domin ka sāke karɓarsa ga zama na har abada.
16 Ba wai ka karɓe shi a matsayin bawa ba, amma har fiye da haka, wato ka karɓe shi a matsayin ɗanˈuwan da ake ƙauna. Ina ƙaunarsa sosai balle ma kai, ai, za ka ƙaunace shi fiye da haka, a matsayinsa na bawa da kuma na wanda ya ba da gaskiya ga Ubangiji!
17 Domin haka idan ni abokin aiki ne a gare ka, to, ka karɓe shi daidai yadda za ka karɓe ni.
18 Idan ma Onisimus ya yi maka laifi, ko yana riƙe da bashinka, ka lissafta duka a kaina.
19 Ni Bulus nake rubuta wannan da hannuna cewa ni zan biya ka. Kada ma in yi zancen sabon rai nan da ka samu ta wurina.
20 Domin haka ɗanˈuwana, ina roƙonka ka yi mini wannan alheri saboda Ubangiji. Ka faranta mini rai cikin Almasihu!
21 Na tabbata za ka yi biyayya. Shi ya sa na rubuta wannan da sani cewa za ka aikata fiye da yadda na faɗa.
22 Har wa yau, ina so ka shirya mini ɗakin da zan sauka, gama ina sa rai cewa ta wurin adduˈoˈinku Allah zai mayar da ni gare ku.
23 Abafaras wanda yake cikin kurkuku tare da ni saboda Almasihu Yesu yana gaishe ka.
24 Markus, da Aristarkus, da Demas, da kuma Luka waɗanda su duk abokan aikina ne, su ma suna gaishe ka.
25 Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă kasance tare da ruhunku. Amin.