Hausa Bible
Matiyu 6
1 “Ku yi hankali kada ayyukan adalcinku yă zama na ganin ido. Domin idan kuka yi haka, ba za ku sami lada a wurin Ubanku na sama ba.
2 “Saboda haka, idan za ka ba da sadaka, kada ka yi ta surutu a kai, yadda munafukai suke yi a majamiˈu da kuma a kan hanyoyi domin mutane su yabe su. Hakika ina gaya muku, sun riga sun sami ladansu ke nan.
3 Amma idan za ka yi wa wani mai bukata sadaka, kada ka bar hannunka na hagu yă san abin da hannunka na dama yake yi,
4 domin sadakar da kake yi ta kasance a ɓoye, Ubanka kuwa da yake ganin dukan abin da ake yi a ɓoye, zai ba ka lada.”
5 “Kuma idan za ku yi adduˈa, kada ku zama kamar munafukai, masu son yin adduˈa a tsaye a cikin majamiˈu da kuma kan hanya domin mutane su gan su. Hakika ina gaya muku, sun riga sun sami ladansu.
6 Amma idan za ka yi adduˈa, ka shiga ɗaki ka rufe ƙofa, ka yi adduˈa ga Ubanka wanda ba a gani, Ubanka kuma wanda yake gani a ɓoye zai ba ka lada.
7 “Idan kuna adduˈa, kada ku yi dogon surutu kamar waɗanda ba su san Allah ba, waɗanda suke tsammani idan suka yi dogon surutu ne za a ji su.
8 Kada ku yi kamarsu, gama Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.
9 Sai ku yi adduˈa kamar haka. “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama, a kiyaye sunanka da tsarki.
10 Mulkinka yă zo, bari a yi nufinka a cikin duniya, kamar yadda ake yinsa a cikin sama.
11 Ka ba mu abincin yau da kullum.
12 Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.
13 Kada ka kai mu cikin jarraba, amma ka tsare mu daga Mugun nan.’
14 “Gama idan kuka gafarta wa waɗanda suka yi muku laifi, Ubanku na sama ma zai gafarta muku.
15 Amma idan kuwa ba ku gafarta wa mutane ba, haka ma Ubanku ba zai gafarta muku laifofinku ba.”
16 “Idan kuna azumi, kada ku ɓata fuska kamar yadda munafukai suke yi. Su dai sukan ɓata fuskarsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Hakika ina gaya muku, sun riga sun sami ladansu ke nan.
17 Amma idan kana azumi, ka wanke fuskarka, ka shafa mai a kanka,
18 domin kada a ga kana azumi. Ubanka wanda ba a gani, wanda kuma yake ganin abin da ake yi a ɓoye, zai ba ka lada.
19 “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya inda gara da tsatsa za su lalatar da ita, inda kuma ɓarayi za su iya shiga su yi sata.
20 Sai dai ku tara wa kanku dukiya a sama, inda gara ko tsatsa ba za su lalatar da ita ba, inda kuma ɓarayi ba za su shiga su yi sata ba.
21 Gama inda dukiyarka take, a can zuciyarka take.
22 “Ido shi ne fitilar jiki, idan idonka yana da lafiya, dukan jikinka ma zai cika da haske.
23 Amma idan idonka ba lafiya, dukan jikinka zai rasa haske. Idan hasken jikinka ya zama duhu, lallai duhun zai yi yawa!
24 “Ba wanda zai iya bauta wa shugabanni biyu, ko dai yă ƙi ɗaya yă so ɗaya, ko yă yi wa ɗayan aminci yă rena ɗayan. Ba dama ku sa ranku ga bin Allah ku kuma sa ga bin kuɗi duk gaba ɗaya.
25 “Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu da yadda za ku rayu game da abin da za ku ci ko abin da za ku sha, ko kuma yadda za ku sami riguna domin jikinku. Rai bai fi abinci ba? Kuma jiki bai fi kayan da za ku sa ba?
26 Ku dubi tsuntsaye mana, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa tara a rumbuna. Duk da haka Ubanku na sama ne yake ciyar da su. Ba ku fi su daraja ba?
27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa zai iya ƙara wa kansa ko awa ɗaya ga kwanakin rayuwarsa?
28 “Kuma don me kuke damuwa game da kayan da za ku sa? Ku dubi fulawar daji yadda suke girma mana, ba sa aiki ko saƙa kome.
29 Duk da haka ina gaya muku, ko Sarki Solomon da dukan darajarsa, bai taɓa ado kamar ɗaya daga cikinsu ba.
30 To, idan har Allah zai yi wa ciyawar daji ado haka waɗanda suke nan yau, gobe kuwa a ƙone su, balle ku? Ya ku marasa bangaskiya!
31 “Saboda haka kada ku damu da cewa, ‘Me za mu ci?’ ko, ‘Me za mu sha?’ ko, ‘Me za mu sa?’
32 Gama waɗanda ba su san Allah ba, su ne suke neman waɗannan abubuwan. Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatar duk waɗannan abubuwan.
33 Muhimmin abu na farko shi ne ku miƙa kanku ga alˈamuran mulkinsa, da kuma aikata adalcinsa, za a kuwa ba ku har da waɗannan abubuwan ma.
34 Saboda haka kada ku damu domin gobe, gama gobe yana zuwa da wahalolinsa, wahalolin yau sun ishe ku domin yau.