Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 20

1 “Mulkin sama kamar wani maigida ne wanda ya fita da sassafe domin yă yi hayar waɗanda za su yi masa aiki a gonarsa ta itatuwan inabi.

2 Da suka shirya a kan kuɗin da ake biyan lebura a yini, sai ya aika su gonarsa.

3 Wajen ƙarfe tara kuma da ya fita, sai ya ga waɗansu suna zaman banza kawai a bakin kasuwa,

4 sai ya ce musu, ‘Ku ma ku je gonata, zan biya ku abin da ya kamata.’ Sai suka tafi.

5 Da ya sāke fita da rana, da kuma wajen ƙarfe uku, ya ɗauki masu aiki.

6 Har yanzu wajen ƙarfe biyar ya sāke fita ya ga waɗansu suna tsaye ba sa yin kome, sai ya ce musu, ‘Don me kuke zaman banza duk yini?’

7 “Suka ce masa, ‘Gama ba wanda ya ba mu aikin yi.’ “Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku je gonata.’

8 “Da yamma ta yi, sai mai gonar ya ce wa mai taimakonsa lura da aikin gonar, ‘Ka kira maˈaikatan ka biya su, ka fara daga na ƙarshe zuwa na farko.’

9 Waɗanda suka je wajen ƙarfe biyar suka zo, kowannensu ya karɓi abin da ya kamata a biya shi a yini.

10 To, waɗanda suka fara zuwa sun yi tsammani za a biya su fiye da sauran, amma su ma kowannensu ya karɓi abin da ya kamata a biya shi a yini.

11 Da suka karɓa, suka yi wa maigidan gunaguni,

12 suna cewa, ‘Waɗanda suka zo daga ƙarshe, aikin awa ɗaya kawai suka yi, ka mai da su daidai da mu, mu da muka yini muna aiki, ga shan rana.’

13 “Sai ya amsa wa ɗaya daga cikinsu ya ce, ‘Abokina, ai, ban cuce ka ba. Ba mu shirya a kan cewa zan biya ka abin da akan biya a yini ba?

14 Ka karɓi abin da yake naka ka tafi. Ni na ga damar in biya waɗanda suka zo daga baya daidai da abin da na biya ka.

15 Ba ni da iko in yi abin da na ga dama da abin da yake nawa? Ko kana jin kishi ne saboda ina da alheri a yalwace?’

16 “Haka na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma za su zama na ƙarshe.”

17 Da Yesu da almajiransa suna haurawa zuwa Urushalima, sai Yesu ya ja su gefen hanya ya ce musu,

18 “Ga shi, za mu je Urushalima. Za a ba da Ɗan Mutum a hannun manyan firistoci da malaman Koyarwar Musa, za su kuma yanke masa hukuncin kisa.

19 Saˈan nan su ba da shi ga waɗanda ba Yahudawa ba, su yi masa baˈa, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.”

20 Saˈan nan sai mamar ˈyaˈyan Zabadi ta zo wurin Yesu da ˈyaˈyanta, ta durƙusa a gabansa ta roƙe shi wani abu.

21 Sai ya ce mata, “Me kike so?” Ta ce masa, “Ka sa waɗannan ˈyaˈyana biyu su zauna, ɗaya a damanka, ɗaya a hagunka, a cikin mulkinka.”

22 Amma Yesu, ya ce wa ˈyaˈyan, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba, za ku iya sha a kwaf na wahalar da zan sha?” Suka ce masa, “Za mu iya.”

23 Ya ce musu, “Lallai za ku sha a kwaf nawa, amma zama a damana ko haguna ba ni nake da ikon bayarwa ba. Ubana na sama ya shirya matsayin nan don waɗanda ya zaɓa.”

24 Da sauran almajiran goma suka ji haka, sai suka ji haushin ˈyanˈuwan nan guda biyu.

25 Amma Yesu ya kira su duka ya ce, “Kun san yadda sarakunan waɗanda ba Yahudawa ba sukan nuna iko a kan mutanensu, manyansu ma suna nuna wa mutanensu iko.

26 Ba zai zama haka a cikinku ba. A maimakon haka duk wanda yake so yă zama babba a cikinku dole ne yă zama mai yi wa sauran hidima.

27 Kuma wanda yake so yă zama shugaba a cikinku, dole ne yă zama bawanku.

28 Haka kuma Ɗan Mutum bai zo domin a bauta masa ba, sai dai domin yă yi bauta, yă kuma ba da ransa domin ceton mutane da yawa.”

29 Da Yesu da almajiransa za su bar Yeriko, mutane da yawa suka bi shi.

30 Sai ga waɗansu makafi biyu suna zaune a gefen hanya. Da suka ji Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Maigirma, Ɗan Dawuda! Ka ji tausayinmu!”

31 Mutane suka yi musu faɗa su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suka ce, “Maigirma, Ɗan Dawuda! Ka yi mana jinƙai!”

32 Sai Yesu ya tsaya ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?”

33 Suka ce masa, “Maigirma, bari mu sami ganin gari.”

34 Saboda tausayi, sai Yesu ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka fara gani, suka bi shi.

Open Bible reader