Hausa Bible
Matiyu 10
1 Sai Yesu ya kirawo almajiransa goma sha biyu, ya ba su iko su fitar da ƙazaman ruhohi su warkar da kowane irin ciwo da rashin lafiya.
2 Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Na farin, Siman wanda ake ce da shi Bitrus, Andarawus ɗanˈuwan Siman, Yakub ɗan Zabadi, Yohanna ɗanˈuwan Yakub,
3 Filibus, Bartalomi, Toma, Matiyu mai karɓar haraji, Yakub ɗan Halfa, Taddiyus,
4 Siman mutumin Kanˈana, Yahuda Iskariyoti wanda ya bashe shi.
5 Yesu ya aiki sha biyun nan ya ce musu, “Kada ku je wurin waɗanda ba Yahudawa ba, kuma kada ku shiga wani garin Samariya,
6 sai dai ku je wurin tumakin da suka ɓata na jamaˈar Israˈila.
7 Yayin da kuke tafiya, ku yi ta yi musu waˈazi cewa, ‘Mulkin sama ya yi kusa.’
8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da waɗanda suka mutu, ku tsabtace masu cutar fatar jiki, ku fitar da aljanu. Kun samu a kyauta, ku kuma bayar kyauta.
9 Kada ku riƙe zinariya, ko azurfa, ko tagulla a aljihunku.
10 Kada kuma ku riƙe jaka, ko riga guda biyu, ko takalma, ko sanda domin tafiyarku, gama maˈaikaci ya cancanci samun abin biyan bukatarsa.
11 “Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mutumin kirki ku zauna da shi har sai lokacin da za ku tashi.
12 Saˈad da kuka shiga gidan, ku ce, ‘Salama a gare ku.’
13 Idan gidan ya cancanta, sai salamarku ta sauka a kansa, amma idan bai cancanta ba, sai salamarku ta komo gare ku.
14 Duk wanda bai karɓe ku ba, ko kuma ya ƙi jin maganarku, ku kakkaɓe ƙurar ƙafafunku saˈad da kuka fita daga gidan ko garin
15 Hakika ina gaya muku, za a fi jin tausayin mutanen Sodom da Gomora fiye da mutanen garin nan a Ranar Shariˈa.”
16 “Ga shi, ina aikanku kamar tumaki cikin kyarketai, saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciya.
17 Ku yi hankali da mutane, gama za su kai ku kotu, su kuma yi muku bulala a majamiˈunsu.
18 Saboda ni kuma, za su kai ku gaban shugabanni da sarakuna, domin ku shaida labari mai daɗi a gabansu da a gaban waɗanda ba Yahudawa ba.
19 Lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da abin da za ku faɗa, gama za a ba ku abin da za ku ce a lokacin.
20 Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.
21 “Ɗanˈuwa zai ba da ɗanˈuwansa a kashe shi, baba kuma yă ba da ɗansa, ˈyaˈya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su.
22 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma wanda ya jimre har zuwa ƙarshe zai tsira.
23 Idan sun tsananta muku a wani gari, ku gudu zuwa gari na gaba, gama hakika ina gaya muku, kafin ku gama zagaya dukan garuruwan Israˈila, Ɗan Mutum zai dawo.
24 “Ba almajiri wanda ya fi malaminsa, ko kuma bawan da ya fi maigidansa.
25 Ya isa almajiri yă zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar maigidansa. Idan suka ce da maigidan Baˈalzabul, me za su ce game da mutanen gidan?”
26 “Saboda haka, kada ku ji tsoronsu, domin ba abin da yake a rufe wanda ba za a bayyana ba, kuma ba abin da yake a ɓoye wanda ba za a sani ba.
27 Abin da nake gaya muku a duhu, ku faɗe shi a haske. Abin da aka faɗa muku a kunne kuwa, ku yi shelarsa daga kan rufin gidaje.
28 Kada ku ji tsoron waɗanda za su iya kashe mutum, amma ba sa iya kashe ransa. Sai dai ku ji tsoron wanda zai iya halaka jiki duk da rai a gidan wuta.
29 Ba ana sayar da ɗan tsuntsu guda biyu kobo ɗaya ba? To, ba ɗayansu wanda zai fāɗi a ƙasa ba tare da sanin Ubanku ba.
30 Ai, ko gashin kanku ma an ƙirga su.
31 Saboda haka, kada ku ji tsoro. Ai, kun fi ɗan tsuntsu daraja sau barkatai.”
32 “Duk wanda ya nuna shi nawa ne a gaban mutane, ni ma zan nuna shi nawa ne a gaban Ubana wanda yake a sama.
33 Amma duk wanda ya yi musūn sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musūn saninsa a gaban Ubana da yake a sama.”
34 “Kada ku yi tsammani na zo in kawo salama ne a duniya. Ba domin in kawo salama na zo ba, sai dai faɗa.
35 Gama na zo ne, “ ‘In sa ɗa yă yi gāba da babansa, ˈya kuma da mamarta, matar ɗa kuma da mamar mijinta.
36 Mutanen gidan mutum ne kuma za su zama abokan gābansa.’
37 “Duk wanda ya fi son mamarsa ko babansa fiye da ni, bai isa yă zama nawa ba. Kuma duk wanda ya fi son ɗansa ko ˈyarsa fiye da ni, bai isa yă zama nawa ba.
38 Duk wanda bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai isa yă zama nawa ba.
39 Duk wanda ya so yă ceci ransa, zai rasa shi. Duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.”
40 “Duk wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, duk wanda ya karɓe ni kuwa ya karɓi wanda ya aiko ni.
41 Duk wanda ya karɓi annabi saboda shi annabi ne, zai sami ladan annabi. Kuma duk wanda ya karɓi mai adalci saboda shi mai adalci ne, zai sami ladan mai adalci.
42 Duk wanda ya ba ɗaya daga cikin mafi ƙanƙantan nan ko da kwaf ɗaya na ruwan sanyi saboda shi almajirina ne, hakika ina gaya muku, ba zai taɓa rasa ladansa ba