Skip to content

Hausa Bible

Markus 1

1 Wannan shi ne labari mai daɗi game da Yesu Almasihu, Ɗan Allah.

2 Ta fara kamar yadda aka rubuta a littafin annabi Ishaya cewa, “Ga shi, na aikar da manzona yă riga ka gaba, wanda zai shirya maka hanya.”

3 Murya mai kira a daji tana cewa, “Ku shirya wa Ubangiji hanya, Ku gyara hanyoyinsa.”

4 Yohanna Mai Baftisma ya kuwa bayyana a daji yana waˈazi cewa mutane su tuba a yi musu baftisma domin a yafe musu zunubansu.

5 Dukan mutanen yankin Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa suna faɗin zunubansu suna tuba. Ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Yodan.

6 Rigar Yohanna kuwa an yi ta da gashin raƙumi ne. Yana kuwa ɗaure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da ruwan zuma.

7 Ya yi waˈazi, ya ce, “Wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni girma, wanda ban isa ko in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba.

8 Na yi muku baftisma da ruwa, amma shi, da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.”

9 Ana nan a cikin kwanakin nan, sai Yesu ya zo daga Nazaret na yankin Galili, sai Yohanna ya yi masa baftisma a Kogin Yodan.

10 Da Yesu yana fitowa daga ruwa, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhun Allah yana saukowa a kansa a kamannin kurciya.

11 Sai aka ji wata murya daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana wanda nake ƙauna. Ina jin daɗinka ƙwarai.”

12 Nan da nan sai Ruhu ya kai Yesu cikin daji,

13 inda ya zauna har kwana arbaˈin. Shaiɗan yana gwada shi. Yesu yana tare da namomin daji, amma malaˈiku suka yi masa hidima.

14 Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, Yesu ya shiga Galili yana shelar labari mai daɗi wanda ya fito daga wurin Allah.

15 Yana cewa, “Lokaci ya cika! Mulkin Allah ya yi kusa! Ku tuba, ku gaskata da labari mai daɗi.”

16 Da Yesu yana wucewa a gefen Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗanˈuwansa Andarawus, suna jefa ragar kamun kifi a teku domin su masu kamun kifi ne.

17 Sai Yesu ya ce musu, “Ku biyo ni, zan mai da ku masu jawo mutane zuwa wurina.”

18 Nan da nan sai suka bar kayansu na kama kifi, suka bi shi.

19 Da ya je gaba kaɗan, sai ya ga Yakub ɗan Zabadi, da ɗanˈuwansa Yohanna, suna cikin jirgin ruwansu suna gyaran ragar kamun kifi.

20 Nan da nan ya kira su, suka kuwa bar babansu Zabadi cikin jirgin tare da leburorin da suka ɗauka, suka bi shi.

21 Yesu da masu binsa suka shiga Kafarnahum. Da Ranar Hutu ta Mako, sai ya shiga majamiˈa yana koyarwa.

22 Suka yi ta mamaki yadda yake koyarwa, domin ya koya musu kamar mutumin da yake da iko, ba kamar malaman Koyarwar Musa ba.

23 Ba labari sai ga wani mutum mai ƙazamin ruhu a cikin majamiˈarsu,

24 yana ihu, yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazaret? Ko ka zo ne ka halaka mu? Na san ko wane ne kai, kai ne Mai Tsarkin nan na Allah!”

25 Sai Yesu ya tsawata wa aljanin, ya ce, “Ka yi shiru! Ka fita daga cikin mutumin nan!”

26 Sai ƙazamin ruhu ya jijjiga mutumin. Ya yi ihu, ya fita daga cikinsa.

27 Duk mutane suka yi mamaki, har suka yi ta tambayar juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa! Wannan mutum yana da iko yă ba ƙazaman ruhohi umarni, suna kuwa yi masa biyayya!”

28 Nan da nan sai labarinsa ya bazu koˈina a kewayen yankin Galili.

29 Da fitarsu daga majamiˈar, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawus, tare da Yakub da Yohanna.

30 Mamar matar Bitrus kuwa tana kwance tana fama da zazzaɓi. Da shigar Yesu, suka ba shi labarinta.

31 Sai ya tafi wurinta, ya kama hannunta ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya bar ta, har ta tashi ta yi musu hidima.

32 Da yamma, bayan fāɗuwar rana, aka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu.

33 Sai dukan mutanen garin suka taru a ƙofar gidan.

34 Ya warkar da marasa lafiya da yawa, masu ciwo iri-iri, ya kuma fitar wa mutane aljanu da yawa. Bai ko yarda aljanun su yi magana ba, domin sun san shi.

35 Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, yă yi adduˈa a can.

36 Sai Siman da waɗanda suke tare da shi suka je nemansa.

37 Da suka same shi, suka ce masa, “Ai, dukan mutane suna nemanka.”

38 Yesu ya amsa ya ce, “Mu je garuruwan da suke gaba, in yi waˈazi a can kuma. Dalilin zuwana ke nan.”

39 Ya zazzaga dukan Galili yana waˈazi a majamiˈunsu, yana kuma fitar wa mutane aljanu.

40 Wani mai cutar fatar jiki ya zo wurin Yesu, ya durƙusa yana roƙo yana cewa, “Idan ka yarda, kana iya ka tsabtace ni in zama marar ƙazanta.”

41 Sai tausayi ya kama Yesu, ya miƙa hannunsa ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, na tsabtace ka, ka zama marar ƙazanta!”

42 Nan da nan sai cutar fatar jikinsa ta bar shi, ya kuwa zama marar ƙazanta.

43 Saˈan nan Yesu ya sallame shi da gargaɗi mai ƙarfi cewa,

44 “Ka lura fa kada ka gaya wa kowa. Amma ka je ka nuna kanka a wurin firist, ka kuma yi hadaya kamar yadda Musa ya ce a yi don tsabtacewa. Ka yi haka don ka tabbatar wa jamaˈa cewa ka warke.”

45 A maimakon haka, sai mutumin ya fita yana ta baza labarin koˈina. Wannan ya sa Yesu bai iya shiga wani gari a fili ba, sai ya dinga zama a waje a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga koˈina.

Open Bible reader