Skip to content

Hausa Bible

Luka 19

1 Yesu ya shiga Yeriko, yana wucewa cikin garin ke nan,

2 sai ga wani shugaban masu karɓar haraji, mai suna Zakka. Shi kuwa mai arziki ne,

3 ya yi ta ƙoƙari yă ga kowane ne Yesun nan, amma bai iya ba domin shi wani ɗan gajere ne, kuma mutane sun yi yawa.

4 Saboda haka sai ya yi gaba da gudu, ya sami wani babban itace ya hau, domin yă gan shi, gama Yesu zai bi ta nan ne.

5 Da Yesu ya kai wurin, sai ya ɗaga kansa sama ya ce, “Zakka, yi maza ka sauko! Yau zan sauka a gidanka.”

6 Zakka ya yi sauri ya sauka, ya karɓe shi da murna.

7 Da jamaˈa suka ga haka, sai duk suka fara gunaguni, suka ce, “Ai! Gidan mai zunubi ne ya sauka!”

8 Sai Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Ka ji nan, maigirma, zan ba da rabin arzikin da nake da shi wa talakawa. Duk wanda kuma na taɓa cutarsa, zan biya shi sau huɗu abin da dā na karɓa.”

9 Sai Yesu ya ce masa, “Yau dai, ceto ya zo gidan nan, tun da shi ma ɗan Ibrahim ne.

10 Gama Ɗan Mutum ya zo ne musamman domin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”

11 Tun suna jin waɗannan abubuwa, Yesu ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, mutane kuma suna tsammani mulkin Allah zai bayyana nan da nan.

12 Sai ya ce musu, “An taɓa yin wani babban mutum wanda za shi wani gari da nisa don a naɗa shi sarki, yă dawo.

13 Kafin yă tafi, ya kira bayinsa guda goma, ya ba kowannensu yawan kuɗin da lebura zai samu cikin wata uku, ya kuma ce musu, ‘Ku yi kasuwanci da su sai na dawo.’

14 Mutanen garinsa kuwa ba sa sonsa. Saboda haka, sai suka aika da ˈyan aika bayan da ya tafi su ce, ‘Ba ma son wannan mutum yă zama sarkinmu.’

15 “Ana nan bayan da aka naɗa mutumin nan sarki, ya dawo gida. Da shigarsa sai ya aika a kira masa duk bayinsa, domin yă san riba nawa suka samu a kan kuɗin da ya bar musu.

16 Na fari ya zo ya ce, ‘Maigirma, na ci riba fam goma daga fam ɗaya da ka ba ni.’

17 Sai maigidan kuma ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan sa ka ka yi mulkin garuruwa goma.’

18 Bawa na biyu ya zo, ya ce, ‘Maigirma, na ci riba fam biyar daga fam ɗaya da ka ba ni.’

19 Maigidan ya ce wa wannan, ‘Za ka yi mulkin garuruwa biyar.’

20 “Wani kuma ya zo, ya ce, ‘Maigirma, ga fam ɗayanka. Na ɗaure shi a ɗan tsumma, na ɓoye.

21 Gama ina jin tsoronka, don kai wani irin mutum ne mai wuyar shaˈani. Ga so na banza a wurinka ba dama, kakan yi girbin abin da ba ka shuka ba.’

22 Sai ya ce masa, ‘Kai wani mugun bawa ne! Zan yi maka shariˈa a kan abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka san cewa ni mutum ne mai wuyar shaˈani, mai so na banza, ina kuma girbin abin da ban shuka ba?

23 To, in ka san haka, me ya sa ba ka sa kuɗina a banki ba, don in na dawo in sami riba a kai?’

24 “Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Karɓi fam ɗayan daga wurinsa a ba bawan nan mai fam goma.’

25 Amma suka amsa masa suka ce, ‘Maigirma, ai, yana da fam goma ko.’

26 Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, gama duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Wanda ba shi da abu kuwa, ko ɗan kaɗan da yake da shi ma, za a karɓa daga gare shi.

27 Waɗannan masu ƙina kuma, waɗanda ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”

28 Da Yesu ya faɗa haka, sai ya yi gaba zuwa Urushalima.

29 Da ya kai kusa da waɗansu ƙauyukan da ake ce da su Betafaji da Betani da suke gefen Tudun Itatuwan Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu,

30 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen nan na gabanku. Da kun kai, za ku ga wani ɗan jakin da ba a taɓa hawa ba a ɗaure. Ku kunce shi ku kawo nan.

31 Idan wani ya ce, ‘Don me kuke kunce jakin?’ Ku ce masa, ‘Mai Girma yana bukatarsa.’ ”

32 Waɗanda aka aika suka tafi, suka kuma sami kome kamar dai yadda Yesu ya gaya musu.

33 Suna cikin kuncewa ke nan, sai masu jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?”

34 Suka ce, “Ai, Mai girma ne yake bukatarsa.”

35 Suka kai shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa rigunansu a kan jakin, sai suka ɗauki Yesu suka sa shi a kai.

36 Yana cikin tafiya, sai mutane suka dinga shimfiɗa rigunansu a kan hanya.

37 Da ya yi kusa da Urushalima, daidai wurin da hanyar ta gangara daga kan Tudun Itatuwan Zaitun, sai taron almajiransa da yawa suka fara gode wa Allah, suna yabonsa da murya mai ƙarfi a kan abubuwa masu ban mamakin da suka gani.

38 Suna cewa, “Albarka ta tabbata ga Sarki wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji! Salama ta kasance a sama, ɗaukaka kuma ga Allah!”

39 Sai waɗansu Farisiyawan da suke cikin jamaˈar suka ce masa, “Malam, ka tsawata wa almajiranka su yi shiru!”

40 Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, duwatsu ma da kansu za su fara ihu.”

41 Da ya zo kurkusa, ya ga birnin Urushalima, sai ya yi mata kuka.

42 Ya ce, “Da ma a ce yau kun san abin da ake bukata domin samun salama! Amma ga shi ba za ku iya gani ba.

43 Lokaci yana zuwa da masu gāba da ku za su gina bango kewaye da ku su yi yaƙi da ku. Sojoji za su kewaye ku ta kowane gefe.

44 Za su yi kaca-kaca da ku, su kuma kashe mutanenku duka. Ba ko dutse ɗaya na gine-ginenku da za a bari a kan ɗanˈuwansa. Wannan zai faru ne saboda ba ku yarda cewa Allah ya zo domin yă cece ku ba.”

45 Sai Yesu ya shiga Haikali ya fara korar masu sayar da kaya,

46 yana ce musu, “Ai, a rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, ‘Gidana zai zama gidan adduˈa.’ Amma kun mai da shi wurin ɓuyan ˈyan fashi!”

47 Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Koyarwar Musa, da shugabannin jamaˈa sun nemi hanyar da za su kashe shi.

48 Amma ba su sami hanyar da za su kashe shi ba domin maganarsa ta ɗauki hankalin kowa da yake a wurin, kuma ba sa so ko kalma ɗaya ta wuce musu.

Open Bible reader