Skip to content

Hausa Bible

Yahaya 14

1 “Kada ku damu. Ku ba da gaskiya ga Allah, ku kuma ba da gaskiya gare ni.

2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa. Idan ba haka ba ne da ba zan faɗa muku wannan ba. Za ni can domin in shirya muku wuri.

3 In kuwa na je na shirya muku wuri, zan dawo in kai ku wurina, domin ku ma ku zauna inda nake.

4 Ai, inda za ni kun san hanya.”

5 Sai Toma ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ai, ba mu san inda za ka ba, yaya za mu san hanyar?”

6 Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.

7 Da kun san ni, da kun san Ubana ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.”

8 Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, in ka nuna mana Uban, to, ai, bukatarmu ta biya ke nan.”

9 Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’?

10 Ba ka ba da gaskiya ba cewa ina cikin Uban, Uban kuma yana cikina? Ai, maganar da nake yi muku ba da ikon kaina ba ne, Uban ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa.

11 Ku gaskata da ni saˈad da na ce ina cikin Uban, Uban kuma yana cikina, ko kuwa ku gaskata da ni saboda ayyukan ban mamakin da na yi.

12 Hakika, ina gaya muku, duk wanda yake ba da gaskiya gare ni, zai yi ayyukan da nake yi. Har ma zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba.

13 Duk dai abin da kuka roƙa cikin sunana zan yi, domin Uban yă sami ɗaukaka ta wurin Ɗan.

14 Ko mene ne kuka roƙa a cikin sunana, zan yi shi.”

15 “In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnaina.

16 Zan kuma roƙi Uba, shi kuwa zai ba ku wani Mai Taimako yă kasance tare da ku har abada.

17 Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya karɓe shi ba don ba ta iya ta gan shi ko ta san shi ba. Amma ku kam kun san shi, don yana zama tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.

18 “Ba zan bar ku kamar marayu ba, zan zo wurinku.

19 Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ina da rai, ku ma za ku rayu.

20 A ranar nan ne fa za ku san cewa ni ina cikin Ubana, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku.

21 Duk wanda ya san umarnaina, yana binsu kuma, shi ne yake ƙaunata. Wanda ya ƙaunace ni kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi in bayyana kaina a gare shi.”

22 Sai Yahuda, ba Iskariyoti ba, ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, amma ba ga sauran duniya ba?”

23 Yesu ya amsa masa ya ce, “Duk wanda yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.

24 Wanda ba ya ƙaunata kuwa, ba ya kiyaye maganata. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.

25 “Duk wannan na faɗa muku ne tun ina tare da ku.

26 Amma Mai Taimako, wato Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, shi ne zai koya muku kome, yă kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.

27 “Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro.

28 “Kun dai ji na ce muku zan tafi, in sāke dawo wurinku kuma. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, gama Uban ya fi ni.

29 To, yanzu na faɗa muku tun bai faru ba, domin a lokacin da ya faru ku ba da gaskiya.

30 Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyar nan yana zuwa, amma ba shi da iko a kaina.

31 Ina yin daidai abin da Uba ya faɗa mini in yi ne domin duniya ta sani ina ƙaunar Uban. Ku tashi mu bar nan.”

Open Bible reader