Skip to content

Hausa Bible

Ibraniyawa 1

1 A zamanin dā, Allah ya yi wa kakanninmu magana ta hanyoyi iri-iri da kuma a lokatai dabam-dabam ta wurin annabawa.

2 Amma a waɗannan kwanakin ƙarshe ya yi mana magana ta wurin Ɗansa. Ta wurin Ɗan ne Allah ya halicci kome da kome. Shi ne kuma ya zama magājin kome.

3 Shi ne hasken ɗaukakar Allah da kuma ainihin kamannin Allah. Daidai yake kuma da Allah. Yana riƙe da dukan kome ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya tsabtace mu daga zunubanmu, sai ya zauna a sama a hannun daman Mai Ɗaukaka duka.

4 Ta haka nan kuma ya sami matsayin da ya fi na malaˈiku kamar yadda sunan da aka ba shi ya fi nasu girma.

5 Gama babu wani malaˈikan da Allah ya taɓa ce masa, “Kai Ɗana ne, yau na zama Ubanka.” Ko kuwa wani da aka ce masa, “Zan zama Ubansa, shi kuwa yă zama Ɗana.”

6 Amma da ya aiki Ɗansa na fari cikin duniya, ya ce, “Bari dukan malaˈikun Allah su yi masa sujada.”

7 Game da malaˈiku, Allah ya ce, “Allah yakan sa malaˈikunsa su zama kamar iska, masu hidimarsa kuma kamar harshen wuta.”

8 Amma game da Ɗan ya ce, “Kujerar mulkinka, ya Allah, na har abada abadin ne, sandan mulkinka na adalci ne.

9 Aikin adalci ne kake so, mugunta kuma ka ƙi sam! Shi ya sa Allah, wato Allahnka, ya keɓe ka, ya shafe ka da man farin ciki, ya girmama ka fiye da abokanka.”

10 Ya kuma ce, “Tun daga farko, ya Ubangiji, kai ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannunka ne.

11 Za su shuɗe, amma kai kana nan dukansu kamar riga za su tsufa.

12 Za ka naɗe su kamar yadi, za a canja su yadda ake canja zane. Amma kai ba ka canjawa, shekarunka marar ƙārewa ne.”

13 Ba wani a cikin malaˈikunsa da Allah ya taɓa ce masa, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin ƙafafunka.”

14 Hakika, dukan malaˈiku ruhohin hidima ne. Allah yakan aike su domin su taimaki waɗanda za su ci gādon ceto.

Open Bible reader