Skip to content

Hausa Bible

Afisawa 3

1 Domin haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku waɗanda ba Yahudawa ba.

2 Na tabbata kun ji labari yadda Allah, a cikin alherinsa, ya ba ni baiwa ta yin hidimar nan don taimakonku,

3 wato, yadda ta wurin ruˈuya Allah ya sanar da ni asirin nufinsa kamar yadda na riga na rubuta labarinsa a taƙaice.

4 Idan kuwa kun karanta wannan, za ku iya gane da abin da na sani game da asirin Almasihu.

5 A zamanin dā ba a gaya wa ˈyan Adam wannan ba, kamar yadda yanzu Allah ya bayyana wa manzanninsa masu tsarki da annabawa masu tsarki ta wurin Ruhu.

6 Asirin shi ne, ta wurin labari mai daɗi na Almasihu Yesu, su waɗanda ba Yahudawa ba sun zama abokan gādo tare da mu Yahudawa. Su da mu mun zama kamar gaɓoɓin jiki ɗaya ne. Su ma suna da rabonsu cikin alkawarin da Allah ya yi mana ta wurin Almasihu Yesu.

7 An kuwa mai da ni mai hidimar wannan labari mai daɗi bisa ga baiwar da aka yi mini, wato alherin da Allah ya ba ni ta wurin ikonsa, ikon da yake aiki a cikina.

8 Ko da yake ni ne mafi ƙanƙanta cikin tsarkaka, ni aka ba wannan baiwa mai daraja, in yi wa waɗanda ba Yahudawa ba waˈazin labari mai daɗin nan a yalwace game da Almasihu, wanda ba a iya yin lissafinsa.

9 Domin kuma in bayyana wa dukan mutane yadda Allah yake aikata shirin nan na asiri wanda shekara da shekaru yake a ɓoye a wurin Allah, wanda ya halicci dukan abubuwa.

10 Nufinsa shi ne yanzu ta wurin jamaˈar masu bi, a sanar da hikimar Allah iri-iri ga masu mulki da ikoki a sammai.

11 Wannan kuwa an yi shi ne bisa ga nufin nan da Allah ya nufa tun daga farko, ya kuma aikata cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

12 Cikinsa ne muke da ƙarfin hali zuwa wurin Allah babu tsoro, da amincewa, ta wurin bangaskiyarmu gare shi.

13 Saboda haka ina roƙonku, kada ku fid da zuciya da ganin dukan wahalar da nake sha dominku. Ai, wahalar nan za ta zama muku abin taƙama.

14 Saboda haka ina durƙusawa a gaban Ubanmu na sama,

15 shi wanda daga wurinsa ne kowane iyali a sama da kuma a nan duniya ya sami ainihin sunansa.

16 Ina roƙonsa yă ba ku baiwa daga cikin yalwar ɗaukakarsa, yă ƙarfafa ku da ikonsa, domin ku zama da ƙarfi a zuciyarku ta wurin Ruhunsa,

17 har ma Almasihu yă zauna a zuciyarku ta wurin bangaskiya. Ina adduˈa cewa ku kafu sosai cikin ƙauna. Bari ƙauna ta zama tushenku,

18 domin ku sami ikon ganewa, ku da dukan sauran tsarkaka, ku fahimci yalwar ƙaunar Almasihu, wato fāɗinta, da tsawonta, da girmanta, da zurfinta.

19 Ku kuma san ƙaunar Almasihu wadda ta fi gaban sani domin ku cika da dukan cikar Allah.

20 Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu wanda ta wurin ikonsa a cikinmu yana aiki har yana aikata abubuwa fiye da dukan abin da za mu roƙa, ko abin da za mu yi tunaninsa.

21 Ɗaukaka ta tabbata a gare shi cikin jamaˈar masu bi da kuma cikin Almasihu Yesu, har zuwa dukan zamanai, har abada abadin. Amin!

Open Bible reader