Skip to content

Hausa Bible

Titus 2

1 Amma kai dai, dole ka koyar da abin da ya dace da koyarwa ta gaskiya.

2 Ka koyar da tsofaffin maza su kame kansu, su natsu, su horar da kansu, su kafu a kan gaskiya cikin bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimrewa.

3 Haka kuma ka koyar da tsofaffin mata su yi rayuwar da ta dace da matan da suke masu bi, ba masu maganar ɓata suna ba, ko masu zaman bayi ga ruwan inabi, amma sai su koyar da abin nagari.

4 Saˈan nan za su horar da mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ˈyaˈyansu,

5 su zama masu kamun kansu, masu tsabtar rai, masu iya kula da iyalansu, masu kirki, masu miƙa kai ga mazansu, domin kada a rena maganar Allah.

6 Haka kuma ka gargaɗi samari su kame kansu.

7 A cikin dukan kome ka nuna kanka mutum ne mai aiki nagari, wanda ya isa abin koyi. Ka yi koyarwarka da gaske tare da ƙwazo,

8 da kuma magana mai maˈana wadda ba za a iya samun abin zargi a cikinta ba. Ta haka za ka ba abokan gābanka kunya yayin da sun rasa mugun abin da za su faɗa a kanmu.

9 Ka umarci bayi su yi biyayya ga iyayengijinsu cikin kome, su kuma sa a ji daɗinsu. Kada su mayar musu da magana,

10 ko su yi musu sata. A maimakon haka, su nuna cewa su masu kirki ne da masu aminci, domin ta haka za a ga darajar koyarwar nan da take game da Allah Mai Cetonmu.

11 Gama alherin Allah ya bayyana, mai kawo ceto ga dukan mutane.

12 Alherin nan yana koya mana mu bar rayuwa marar halin Allah, da shaˈawace-shaˈawacen duniya, mu kame kanmu, mu zama masu gaskiya a zuci, muna masu halin Allah a wannan duniya.

13 Mu yi zaman haka yayin da muke jira cikawar sa zuciyar nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu mai girma da Mai Ceto Yesu Almasihu.

14 Yesu ne ya bayar da kansa domin yă fanshe mu daga dukan mugunta, domin yă tsabtace wa kansa jamaˈa ta musamman waɗanda suke da ƙwazon yin ayyukan kirki.

15 Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka ƙarfafa masu jinka, ka kuma tsawata musu da dukan iko. Kada ka yarda wani yă rena ka.

Open Bible reader