Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 5

Da Yesu ya ga mutane sun taru da yawa, sai ya hau kan tudu ya zauna. Almajiransa kuma suka zo wurinsa,

sai ya buɗe baki ya fara koya musu.

1 “Masu albarka ne waɗanda suka san kāsawarsu ta ruhu, gama mulkin sama nasu ne.

2 Masu albarka ne masu baƙin ciki, gama za a yi musu taˈaziyya.

3 Masu albarka ne masu tawaliˈu, gama za su gāji duniya.

4 Masu albarka ne masu jin yunwa da ƙishin yin adalci, gama za a ƙosar da su.

5 Masu albarka ne masu nuna jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.

6 Masu albarka ne masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.

7 Masu albarka ne masu sada zumunci, gama za a ce da su ˈyaˈyan Allah.

8 Masu albarka ne masu shan tsanani saboda adalci, gama mulkin sama nasu ne.”

9 “Masu albarka ne ku, saˈad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma yi muku mugunta iri-iri saboda ni.

10 Ku yi murna da farin ciki sosai, domin za ku sami lada mai yawa a sama, gama haka mutane suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.”

11 “Ku ne gishirin duniya. Amma idan gishiri ya rabu da daɗinsa, ta yaya za a mai da daɗinsa? Zai zama ba shi da sauran amfani sai dai a zubar da shi, a tattaka shi.

12 “Ku ne hasken duniya. Ai, birnin da aka gina a kan tudu ba a iya ɓoye shi.

13 Ba a kunna fitila a rufe ta da kwano, sai dai a ajiye ta a kan sanda mai riƙe fitilu inda za ta ba da haske ga dukan mutanen gidan.

14 Haka kuma, bari ku zama masu haske ga mutane, domin idan suka ga ayyuka masu kyau da kuke yi, za su ɗaukaka Ubanku wanda yake cikin sama.

15 “Kada ku yi tsammani na zo ne in rushe Koyarwar Musa da littattafan annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, sai dai domin in cika su.

16 Hakika ina gaya muku, har sai sama da ƙasa sun shuɗe, ba wani layi ko ɗigo na Koyarwar Musa wanda zai shuɗe, sai an cika kome duka.

17 Saboda haka duk wanda ya karya ko da ɗaya daga cikin ƙananan dokokin nan, ya kuma koya wa mutane su karya dokokin, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a cikin mulkin sama. Duk wanda ya bi su kuwa har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a mulkin sama.

18 Ina gaya muku idan ba ku fi malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa adalci ba, ba za ku shiga mulkin sama ba, ko kaɗan.

19 “Kun dai ji an faɗa wa kakanninmu cewa, ‘Kada ka kashe wani, wanda ya kashe wani kuma, za a hukunta shi.’

20 Amma ina gaya muku, wanda yake fushi da ɗanˈuwansa, za a hukunta shi. Wanda ya kira ɗanˈuwansa banza, za a kai shi kotu. Wanda kuma ya kira ɗanˈuwansa wawa, ya dace da gidan wuta.

21 Saboda haka, idan kana cikin ba da baiko a kan bagaden hadaya, a nan ka tuna cewa ɗanˈuwanka yana da wata damuwa game da kai,

22 sai ka ajiye baikonka a gaban bagaden tukuna, ka je ka shirya da ɗanˈuwanka. Saˈan nan ka zo ka ba da baikonka.

23 “Idan wani ya kai ƙararka, ka yi sauri ka shirya da shi tun kuna kan hanya kafin ku isa kotu. Idan ba haka ba kuwa zai haɗa ka da alƙali, alƙali kuma yă haɗa ka da ɗan sanda a kuma kulle ka a kurkuku.

24 Gaskiya ina gaya maka, kafin a fitar da kai daga nan, sai ka biya dukan kuɗin da ake binka.

25 “Kun dai ji an faɗa cewa, ‘Kada ka yi zina.’

26 Amma ina faɗa muku cewa, idan mutum ya yi wa mace kallon shaˈawa, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.

27 Idan idonka na dama yana sa ka ka yi zunubi, ka cire shi ka yar. Gara ka rasa wata gaɓa ta jikinka da a jefa dukan jikinka a cikin gidan wuta.

28 Idan hannunka na dama yana sa ka ka yi zunubi, ka cire shi ka yar. Gara ka rasa wata gaɓa ta jikinka da a jefa jikinka ɗungum a cikin gidan wuta.

29 “An kuma faɗa cewa, ‘Wanda ya saki matarsa dole yă ba ta takardar saki.’

30 Amma abin da nake gaya muku shi ne, idan mutum ya saki matarsa ba domin laifin yin zina ba, ya sa ta a hanyar yin zina ke nan. Duk wanda ya aure ta kuma, ya yi zina.

31 “Har yanzu dai kun ji an faɗa wa kakanninku cewa, ‘Kada ka yi rantsuwar ƙarya, sai dai ka cika rantsuwar da ka yi wa Ubangiji.’

32 Amma abin da nake gaya muku shi ne, kada ku rantse sam, ko da sama, domin wurin zaman Allah ke nan.

33 Kada kuma ku rantse da ƙasa, domin nan ne Allah yake sa ƙafarsa, ko kuma da Urushalima domin ita ce birnin babban Sarki.

34 Kada kuwa ka rantse da kanka domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba.

35 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, ‘I’ ko ‘Aˈa’, abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.

36 “Kun dai ji an faɗa cewa, ‘Ido a maimakon ido, haƙori kuma a maimakon haƙori.’

37 Amma abin da nake faɗa muku shi ne, kada ku ƙi wanda ya yi muku laifi. Idan wani ya mare ka a kumatun dama, ka juya masa ɗayan yă mara.

38 Idan wani ya kai ƙararka domin yă ƙwace rigarka, to, ka ba shi har da mayafinka ma.

39 Idan wani mai iko ya matsa maka ku yi tafiyar kilomita ɗaya, to, ku yi tafiyar kilomita biyu.

40 Idan wani ya roƙe ka abu, ka ba shi. Wanda kuma ya zo neman aro daga wajenka, kada ka hana shi.

41 “Kun dai ji an faɗa cewa, ‘Ka ƙaunaci ɗanˈuwanka, ka ƙi wanda ba ya ƙaunarka.’

42 Amma abin da nake gaya muku shi ne, ku ƙaunaci waɗanda ba sa ƙaunarku, ku yi wa masu tsananta muku adduˈa.

43 Ta yin haka ne za ku zama ˈyaˈyan Ubanku na sama, wanda yake sa rana ta yi haske a kan masu kirki da marasa kirki ma, yă kuma aiko ruwan sama a kan masu adalci da marasa adalci.

44 Idan waɗanda suke ƙaunarku kawai kuke ƙauna, wane lada za ku samu? Ko masu karɓar haraji ma, ai, suna yin haka.

45 Idan kuwa ˈyanˈuwanku kawai kuke gai da su, to, me kuke yi wanda ya fi na waɗansu? Ai, ko waɗanda ba Yahudawa ba ma suna yin haka.

46 Saboda haka sai ku zama cikakku kamar yadda Ubanku na sama yake cikakke.

Open Bible reader