Skip to content

Hausa Bible

Matiyu 24

1 Da Yesu ya fita daga cikin Haikali yana tafiya, sai almajiransa suka nuna masa gine-ginen Haikalin.

2 Sai ya tambaye su ya ce, “Kun ga dukan waɗannan gine-gine? Hakika ina gaya muku, ba dutse ko ɗaya da za a bari a kan wani. Duka za a rushe su.”

3 Yesu yana zaune a kan Tudun Itatuwan Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa su kaɗai suka ce, “Faɗa mana, yaushe ne wannan zai faru? Kuma mece ce alamar dawowarka da kuma ta ƙarshen zamani?”

4 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku lura fa, kada kowa yă ruɗe ku.

5 Gama mutane da yawa za su zo a cikin sunana, za su ce, ‘Ni ne Almasihu’, har su ruɗi mutane da yawa.

6 Za ku kuma ji labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu. Kada ku ji tsoro, domin dole ne haka yă faru, amma ƙarshen bai zo ba tukuna.

7 Alˈumma za ta tasar wa alˈumma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da rawar ƙasa a wurare dabam-dabam.

8 Amma wannan duka masomin azaba ne kawai.

9 “Saˈan nan za su ba da ku ga azaba, su kuma kashe ku. Duniya duk za ta ƙi ku saboda sunana.

10 Saˈan nan mutane da yawa za su yi sanyi a cikin bangaskiyarsu, su bashe juna, su kuma ƙi juna.

11 Annabawan ƙarya kuma za su taso da yawa, su ruɗi mutane da yawa.

12 Saboda yawan mugunta, ƙaunar da yawancin mutane suke yi wa juna za ta ragu.

13 Amma wanda ya jimre har zuwa ƙarshe, zai tsira.

14 Kuma za a ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan alˈummai, saˈan nan ƙarshen yă zo.

15 “Za ku ga abin ƙazanta mai kawo halakarwa, wanda annabi Daniyel ya faɗa, yana tsaye a Wuri Mai Tsarki. Bari mai karatu yă gane.

16 To, sai waɗanda suke cikin yankin Yahudiya su gudu zuwa cikin duwatsu.

17 Wanda yake kan rufin ɗaki kada yă sauko wai zai ɗauki abin da yake cikin gida.

18 Wanda yake a gona kuma kada yă koma wai zai ɗauki mayafinsa.

19 Kaiton mata masu ciki, da masu goyo a wannan lokaci!

20 Ku yi adduˈa kada gudun nan yă zo muku a lokacin sanyi ko Ranar Hutu ta Mako.

21 Gama a lokacin za a yi wata azaba mai zafi irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinta ba.

22 Da ba don an rage kwanakin nan ba, da ba ɗan Adam wanda zai tsira. Amma saboda waɗanda aka zaɓa za a rage kwanakin.

23 “A lokacin nan, ko wani ya ce muku, ‘Duba, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Ga shi can!’ kada ku yarda.

24 Gama almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su fiffito, su yi manyan alamu da ayyukan ban mamaki domin su ruɗe mutane, har da waɗanda aka zaɓa in zai yiwu.

25 To, na dai gaya muku tun da wuri.

26 “Domin haka idan aka ce muku, ‘Ga shi can a daji,’ kada ku fito. Idan aka ce muku, ‘Yana can cikin ɗaki a ɓoye,’ kada ku yarda.

27 Gama kamar yadda walƙiya take haskakawa daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum za ta kasance.

28 “Inda gawa take, ai, a nan ungulaye suke taruwa.

29 “Nan da nan bayan kwanakin azabar nan, “ ‘Sai rana za ta yi duhu, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari za su faffāɗi daga sama, za a kuma girgiza ikokin sararin sama.’ ”

30 “Saˈan nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama. Duk kabilun duniya kuma za su yi kuka saboda tsoro. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin girgije da iko da ɗaukaka mai yawa.

31 Zai kuwa aiko malaˈikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, su kuma tattaro waɗanda aka zaɓa daga gabas da yamma da kudu da arewa, wato daga wannan iyakar duniya zuwa wancan.”

32 “Ku koyi wani abu daga itacen ɓaure. Idan rassansa sun fara sākewa, suna fitar da sabon ganye, kun san damina ta yi kusa ke nan.

33 Haka kuma idan kuka ga duk abubuwan nan da na gaya muku, ku san cewa lokaci ya yi kusa, yana dab da bakin ƙofa.

34 Hakika ina gaya muku, mutanen zamanin nan ba za su mutu ba, sai duk abubuwan nan sun faru.

35 Sama da duniya za su ƙāre, amma kalmata ba za ta ƙāre ba ko kaɗan.”

36 “Amma ba wanda ya san ranar ko a ƙarfe nawa ne wannan zai faru, ko malaˈikun da suke sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.

37 Kamar yadda aka yi a kwanakin Nuhu, haka zai kasance a dawowar Ɗan Mutum.

38 Kamar a lokacin nan kafin babbar ambaliyar ruwan, ana ci, ana sha, maza suna aure, ana ba da mata ga aure, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgin.

39 Kafin su san abin da ake ciki, babbar ambaliyar ruwa ta zo ta kwashe su duka. Haka kuwa dawowar Ɗan Mutum za ta kasance.

40 A lokacin nan, mutum biyu za su kasance a gona, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗaya.

41 Mata biyu za su kasance suna niƙa tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗaya.

42 “Domin haka sai ku zauna da shiri, gama ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.

43 Amma ku dai sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne ɓarawo zai zo da dare, da ba zai yi barci ba, kuma ba zai bari a shiga gidansa ba.

44 Domin haka ku ma sai ku zauna da shiri, domin a lokacin da ba ku yi tsammani ba, shi ne Ɗan Mutum zai zo.”

45 “Wane ne bawan nan mai aminci, mai hikima, wanda maigidansa ya sa shi yă lura da gidansa, yake kuma ba sauran bayi abincinsu a kan lokaci?

46 Mai albarka ne bawan da maigidansa zai zo yă same shi yana yin aikinsa.

47 Hakika ina gaya muku, zai sa wannan bawa yă lura masa da kayansa duka.

48 Amma mai yiwuwa bawan mugu ne, zai kuma ce wa kansa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba,’

49 saˈan nan yă fara dūkan abokan aikinsa, yana ci, yana sha tare da masu buguwa.

50 Idan ya yi haka, maigidansa zai zo a ranar da bai yi tsammani ba, a kuma lokacin da bai sani ba,

51 maigidan zai yi masa mugun dūka, yă kuma hukunta shi tare da munafukai. A wurin nan za a yi kuka da cizon haƙora.”

Open Bible reader