Hausa Bible
Matiyu 15
1 Ana nan sai Farisiyawa da malaman Koyarwar Musa suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka ce,
2 “Don me almajiranka suke karya alˈadar dattawa? Gama ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.”
3 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku fa, don me kuke karya dokokin Allah saboda alˈadarku?
4 Ai, Allah ya ce, ‘Ka girmama babanka da mamarka,’ kuma ‘Duk wanda ya zagi babansa ko mamarsa lallai a kashe shi.’
5 Amma kukan koya cewa idan mutum yana da wani abin da zai taimaki babansa ko mamarsa da shi, amma sai ya ce, ‘Duk abin da dā za ku samu a wurina, na keɓe wa Allah,’ to, ba lallai ke nan yă ba iyayensa girma ba.
6 Wato, saboda alˈadarku, kun mai da maganar Allah banza.
7 Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce,
8 “ ‘Mutanen nan fa, da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.
9 A banza ne suke yi mini sujada, suna koyar da dokokin mutane a matsayin kalmar Allah.’ ”
10 Yesu ya kira taron mutane ya ce musu, “Ku saurara ku gane.
11 Ba abin da yake shiga bakin mutum ne yakan ƙazantar da shi a gaban Allah ba, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa.”
12 Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce masa, “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganar nan?”
13 Yesu ya amsa ya ce, “Duk shukar da ba Ubana na sama ne ya shuka ba, za a tumɓuke shi.
14 Bar su kawai. Su makafi ne masu yi wa makafi jagora. Idan kuwa makaho ya yi wa wani makaho jagora, ai, dukansu za su fāɗi cikin rami.”
15 Amma Bitrus ya ce masa, “Ka bayyana mana wannan misali.”
16 Sai Yesu ya ce, “Ashe, har yanzu ba ku gane ba?
17 Ina nufin duk abin da mutum ya ci, da farko zai shiga bakinsa, saˈan nan zai shiga cikinsa, kuma daga ƙarshe zai fita daga jikinsa.
18 Amma abin da yake fitowa daga baki, daga zuciya yake fitowa. Shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum a gaban Allah.
19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani suke fitowa. Wato, su kisan kai, da zina, da lalata, da sata, da shaidar ƙarya, da ɓata suna.
20 Waɗannan suke ƙazantar da mutum a gaban Allah, amma cin abinci da hannun da ba a wanke ba, ba ya ƙazantar da mutum a gaban Allah.”
21 Yesu ya bar wurin ke nan ya tafi yankin biranen Taya da Sidon,
22 sai ga wata ˈyar ƙasar Kanˈana ta zo ta ɗaga murya ta ce, “Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, Ɗan Dawuda. Wani aljani yana ba ˈyata wahala.”
23 Yesu bai ce mata kome ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Ka kore ta! Domin tana binmu tana damunmu da ihu!”
24 Ya amsa ya ce, “An aiko ni ne domin tumakin Israˈila waɗanda suka ɓata, ba domin waɗansu ba.”
25 Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni.”
26 Ya amsa ya ce, “Ba zai yi kyau a ɗauki abincin yara a ba karnuka ba.”
27 Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko karnuka ma sukan lashe sauran abincin da yake fāɗuwa daga teburin masu gidan.”
28 Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Uwargida, bangaskiyarki tana da ƙarfi, bari bukatarki ta biya.” Nan take ˈyarta ta warke.
29 Daga wurin Yesu ya bi ta gefen Tekun Galili. Saˈan nan ya hau tudu ya zauna.
30 Mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka zo da guragu, da makafi, da masu dungu, da bebaye, da waɗansu da yawa, suka ajiye su a gabansa. Ya kuwa warkar da su.
31 Har mutane suka yi mamaki da suka ga bebaye suna magana, masu dungu kuma gaɓoɓinsu suna aiki, guragu suna tafiya, makafi kuma suna gani. Sai duk suka ɗaukaka Allah na Israˈila.
32 Ana nan sai Yesu ya kira almajiransa ya ce, “Ina jin tausayin jamaˈar nan, gama yau kwana uku ke nan suna tare da ni, kuma ba su da abinci. Bāna so in sallame su da yunwa, domin za su iya suma a hanya.”
33 Sai almajiran suka ce masa, “A daji haka, ina za mu sami burodin da zai isa mu ciyar da wannan jamaˈa?”
34 Yesu ya tambaye su ya ce, “Burodi nawa kuke da shi?” Suka ce, “Guda bakwai da ƙananan kifaye kaɗan.”
35 Sai ya sa taron mutanen su zauna a ƙasa,
36 ya ɗauki burodin nan bakwai da kifayen. Da ya yi godiya ga Allah, sai ya rarraba su, ya ba almajiran, almajiran suka ba taron mutanen.
37 Kowa ya ci ya ƙoshi, almajiran kuwa suka tara ragowar abincin, cike da kwanduna bakwai.
38 Mutanen da suka ci kuwa sun kai maza dubu huɗu, ban da mata da yara.
39 Bayan da ya sallami taron mutanen, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi yankin Magadan.