Skip to content

Hausa Bible

Markus 3

1 Da Yesu ya sāke shiga cikin majamiˈa, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu a cikin majamiˈar.

2 Waɗansu mutane kuwa suna neman hanya su sami Yesu da laifi, saboda haka sai suka zuba ido su ga ko Yesu zai warkar da mutumin a Ranar Hutu ta Mako.

3 Sai Yesu ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito ka tsaya nan gaba.”

4 Saˈan nan Yesu ya tambaye su ya ce, “Mene ne ya dace a yi a Ranar Hutu ta Mako? A yi alheri ko a yi mugunta? A ceci rai, ko a kashe rai?” Amma mutanen suka yi shiru.

5 Yesu ya duddube su cikin fushi, yana kuma baƙin ciki domin taurin zuciyarsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Ka miƙe hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya warke nan da nan.

6 Da ganin haka kuwa Farisiyawa suka fita daga majamiˈar. Nan da nan suka yi shawara da mutanen Hirudus a kan yadda za su kashe Yesu.

7 Sai Yesu ya tashi tare da almajiransa, suka bar garin suka je bakin Tekun Galili. Sai mutane da yawan gaske daga Galili suka bi shi, har da mutanen Yahudiya,

8 da na Urushalima, da na yankin Edom, da na ƙetaren Kogin Yodan, da kuma mutanen wajen Taya da kuma Sidon. Da yawansu suka zo saboda sun ji dukan abin da yake yi.

9 Don gudun kada mutane su matse shi, sai Yesu ya faɗa wa almajiransa su kawo masa ƙaramin jirgin ruwa ɗaya.

10 Ya yi haka domin ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu ciwo suna ta zuwa kusa da shi domin su taɓa shi.

11 Duk lokacin da ƙazaman ruhohi suka gan shi, sai su fāɗi a gabansa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne.”

12 Amma ya umarce su kada su gaya wa kowa wane ne shi.

13 Ana nan, sai Yesu ya hau babban tudu, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa.

14 Saˈan nan ya zaɓi mutum sha biyu daga cikinsu su kasance da shi. Yana so ya dinga aikarsu su yi waˈazi,

15 su kuma sami ikon fitar da aljanu.

16 Ga sha biyun da ya zaɓa. Siman, wanda Yesu ya sa masa suna Bitrus,

17 Yakub ɗan Zabadi da ɗanˈuwansa Yohanna, waɗanda ya sa musu suna Buwarnajis, wato ˈyaˈyan tsawa,

18 Andarawus, Filibus, Bartalomi, Matiyu, Toma, Yakub ɗan Halfa, Taddiyus, Siman mutumin Kanˈana,

19 Yahuda Iskariyoti wanda ya bashe shi.

20 Saˈan nan Yesu ya shiga wani gida, mutane kuma suka sāke haɗuwa har shi da almajiransa ba su iya cin abinci ba.

21 Da ˈyanˈuwansa suka ji haka, sai suka tafi domin su kama shi, saboda mutane suna cewa, “Ai, ya haukace!”

22 Malaman Koyarwar Musa kuwa da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, Baˈalzabul sarkin aljanu ne ya shiga cikinsa! Da ikonsa kuma yake fitar da aljanu.”

23 Sai Yesu ya kira mutanen, ya yi musu misalai cewa, “Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan kuma?”

24 Ai, idan mulki ya rabu, ɗaya gefen yana gāba da ɗayan, wannan mulki ba zai tsaya ba.

25 Haka kuma idan gida ya rabu biyu, ɗaya gefen yana gāba da ɗayan, wannan gida ba zai tsaya ba.

26 Idan Shaiɗan kuma ya tayar wa kansa ya kuma rabu, ba zai tsaya ba. Ƙarshensa ya zo ke nan.

27 “Ba wanda zai iya shiga gidan mutum mai ƙarfi ya kwashi kayansa, sai dai ya fara kama mutumin, ya ɗaure. Saˈan nan zai iya kwashi kayan gidansa.

28 “Ina faɗa muku gaskiya, za a yafe wa mutane kowane irin zunubi, da maganar saɓo ga Allah da suka yi.

29 Amma fa, duk wanda ya yi maganar saɓo game da Ruhu Mai Tsarki ba za a taɓa yafe masa ba har abada. Ya yi zunubi na har abada ke nan.”

30 Yesu ya faɗa wannan ne kuwa don sun ce, “Yana da ƙazamin ruhu ne.”

31 Sai mamar Yesu da ˈyanˈuwansa suka zo. Suka tsaya a waje suka aika wani yă kira shi.

32 Mutane kuwa suna zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga mamarka da ˈyanˈuwanka suna nemanka a waje.”

33 Sai ya tambaye su ya ce, “Su wane ne mamata da ˈyanˈuwana?”

34 Ya duddubi waɗanda suke zaune kewaye da shi, sai ya ce, “Ga mamata da ˈyanˈuwana!

35 Ai, duk wanda ya yi abin da Allah yake so, shi ne ɗanˈuwana, ita ce ˈyarˈuwata, ita ce kuma mamata.”

Open Bible reader