Hausa Bible
Luka 17
1 Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da za su sa mutane su yi zunubi. Amma kaiton wanda ya zama dalilin kawo su!
2 Da wani yă sa ɗaya daga cikin yara ƙananan nan yă yi zunubi, gara a ɗaura babban dutsen niƙa a wuyansa a jefa shi cikin teku.
3 Ku lura da kanku fa. “Idan ɗanˈuwanka ya yi maka laifi, ka yi masa magana. In ya nemi gafara, ka yafe masa.
4 Ko da ya yi maka laifi sau bakwai wato, ba iyaka a rana ɗaya, in har ya dinga cewa, ‘Na yi laifi, ka yafe mini,’ sai ka yafe masa.”
5 Sai manzanni suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya.”
6 Ubangiji ya amsa musu ya ce, “Idan kuna da bangaskiya da ta kai ko da misalin ƙwayar mastad, wadda ta fi ƙanƙanta ciki iri duka za ku ce wa wannan babban itace, ‘Ka bar nan, ka je ka tsaya a can cikin teku!’ Zai kuma bi abin da kuka ce yă yi.
7 “Misali, a ce ɗaya daga cikinku yana da bawa wanda yake yi masa noma ko kuwa kiwon tumaki. Wane ne a cikinku in ya dawo daga gona zai ce masa, ‘Yi maza, ka zo ka zauna, ka ci abinci?’
8 A maimakon haka ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma tukuna, ka kawo mini in ci in sha, kafin ka ci naka, ba?’
9 Za a gode wa bawa saboda ya yi aikin da ya kamata yă yi ne?
10 Haka ku ma, idan kuka bi duk abin da aka ce muku ku yi, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta. Mu dai muna yin abin da ya kamata mu yi ne kawai.’ ”
11 Da Yesu ya kama hanya zai je Urushalima, sai ya bi kan iyakar da take tsakanin Samariya da Galili.
12 Zai shiga wani ƙauye ke nan sai ga masu cutar fatar jiki guda goma suka tsaya da nisa
13 suka ɗaga murya suka ce, “Ya Yesu Maigirma! Ka ji tausayinmu!”
14 Da Yesu ya gan su, sai ya ce musu, “Ku je wurin firistoci su gan ku.” Suna kan hanyar tafiya ke nan sai suka zama marasa ƙazanta.
15 Da ɗayansu ya ga an warkar da shi, sai ya koma, yana yabon Allah da murya mai ƙarfi.
16 Ya zo ya rusuna da fuskarsa har ƙasa a gaban Yesu, ya gode masa. Shi mutumin nan Basamariye ne.
17 Yesu ya ce, “Ba mutane goma ne aka tsabtace su ba? Ina sauran taran?
18 Me ya sa sai baƙon nan ne kaɗai ya dawo domin yă yi wa Allah godiya?”
19 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi ka tafi abinka, bangaskiyarka ce ta sa ka warke.”
20 Da waɗansu Farisiyawa suka tambayi Yesu lokacin da mulkin Allah zai zo, sai ya ce musu, “Ai, zuwan mulkin Allah ba da ido ake ganinsa ba.
21 Ba wanda zai ce, ‘Ai, ga shi nan,’ ko kuma ‘ga shi can.’ Domin mulkin Allah yana nan a cikinku.”
22 Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa inda za ku yi marmarin ganin rana ɗaya daga cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.
23 Mutane za su ce muku, ‘Duba can,’ ko kuma, ‘Duba nan.’ Amma kada ku je ku duba.
24 Ranar da Ɗan Mutum zai sāke zuwa, zai zo kamar walƙiyar da take haskakawa daga wannan iyakar duniya zuwa wancan.
25 Amma sai ya fara shan wahala iri-iri tukuna, har mutanen zamanin nan su ƙi shi.
26 Kamar yadda dai ya faru a zamanin Nuhu, haka ne zai faru a lokacin da Ɗan Mutum zai dawo.
27 Mutane suka dinga ci da sha, maza suna aure, ana ba da mata ga aure har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, babbar ambaliyar ruwa kuma ta zo ta halaka su duka.
28 Haka ma aka yi a lokacin Lot. Ana ci ana sha, ana saya ana sayarwa, ana shuke-shuke, ana kuma gine-gine.
29 Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, aka zuba wuta da farar wuta mai wari daga sama, aka kakkashe su duka.
30 Haka zai zama a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana.
31 “A ranar nan fa, wanda yake kan rufin ɗaki kada yă sauko wai zai kwashi kayansa a cikin gida. Haka ma duk wanda ya je gona, kada yă koma gida.
32 Ku tuna fa da matar Lot!
33 Duk wanda yake so yă kiyaye ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai kiyaye shi.
34 Ina gaya muku, a daren da wannan zai faru za a ga mutane biyu suna kwance a gado ɗaya za a ɗauki ɗaya a bar ɗaya.
35 Mata biyu za su kasance suna niƙan dawa tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗaya.
36 Mutum biyu za su kasance a gona, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗaya.”
37 Sai almajiran suka tambaye shi, suka ce, “Ina ne, Ubangiji?” Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulaye suke taruwa.”