Skip to content

Hausa Bible

Luka 15

1 Wata rana masu karɓar haraji da masu zunubi suka zo domin su ji koyarwar Yesu.

2 Sai Farisiyawa da malaman Koyarwar Musa suka fara gunaguni suna cewa, “Haba! Wannan mutum ya mai da kansa abokin masu zunubi, har ma yana cin abinci da su.”

3 Sai Yesu ya ba su wannan misali.

4 “A ce ɗayanku yana da tumaki ɗari, sai ɗayansu ta ɓace, ai, zai bar casaˈin da taran a inda suke kiwo, yă je neman wannan da ta ɓace.

5 Idan ya same ta, zai yi murna, yă ɗauke ta a kafaɗa

6 yă kai ta gida. Saˈan nan yă kira abokansa da kuma waɗanda suke zama tare da shi, yă ce musu, ‘Ku taya ni murna gama na sami wannan tunkiyar da ta ɓace!’

7 Ina dai gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama a kan mai zunubi guda ɗaya wanda ya tuba, fiye da masu adalci casaˈin da tara, waɗanda ba sa bukatar tuba.

8 “A ce, mace tana da kuɗin azurfa guda goma, ɗaya ya ɓata, ai, za ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nemansa sai ta same shi.

9 Idan ta same shi, sai ta tara abokanta da waɗanda suke zama tare da ita, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, don na sami kuɗin nan da ya ɓace.’

10 Ina gaya muku, haka zai zama abin murna ga malaˈikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”

11 Sai Yesu ya ce, “An taɓa yin wani mutum wanda yake da yara maza biyu.

12 Ƙaramin ɗa a cikinsu ya ce wa babansu, ‘Baba, ni a ba ni yanzu abin da aka shirya za a ba ni bayan ka mutu.’ Sai baban ya raba musu dukiyarsa.

13 Bayan ˈyan kwanaki, sai ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya bar gida. Ya je wani gari mai nisa. A can ne ya je ya yi banza da kuɗin cikin iskanci.

14 Bayan da ya cinye duk abin da yake da shi, sai muguwar yunwa ta shiga wannan garin, shi kuwa ya shiga cikin rashi.

15 Sai ya je ya nemi aiki a wurin wani mutumin ƙasar, sai mutumin ya tura shi yă yi kiwon aladunsa.

16 Ya nemi dusar da aladun suke ci domin yă ci, amma ba wanda ya ba shi.

17 A ƙarshe sai ya dawo ciki hankalinsa, sai ya ce, ‘Kai! Ga maˈaikatan babana duk suna banza da abinci, a ce ga ni zan mutu da yunwa!

18 Zan tashi in koma wurin babana in ce, “Baba, na yi wa Allah laifi, na kuma yi maka.

19 Ban ma isa a ƙara kirana ɗanka ba. Ka sa ni in zama kamar ɗaya daga cikin maˈaikatanka.” ’

20 Sai ya tashi ya kama hanya zai koma wurin babansa. “Tun yana daga nesa, sai babansa ya gane shi. Tausayi ya kama baban, ya tashi da gudu, ya je ya rungumi ɗansa, ya yi ta yin masa sumba.

21 Sai ɗan ya ce, ‘Baba, na yi wa Allah laifi na kuma yi maka. Ban isa a ƙara kirana ɗanka ba.’

22 “Amma baban ya kira bayinsa, ya ce, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau, ku sa masa. Ku sa masa zobe da takalma,

23 a kuma kawo saniyar nan mai ƙiba a yanka, mu ci, mu yi murna.

24 Domin ɗan nan nawa, dā ya mutu amma yanzu ya dawo. Dā ya ɓace, amma yanzu an same shi.’ Sai suka yi murna sosai.

25 “To, a wannan lokaci dai babban ɗansa wanda ya je gona yana dawowa. Da ya yi kusa da gida, sai ya ji ana buga ganga, ana rawa.

26 Sai ya kira wani bawan gidan, ya tambaye shi abin da yake faruwa.

27 “Bawan ya ce, ‘Ai, ƙanenka ne ya dawo, shi ne babanka ya sa aka yanka saniya mai ƙibar nan saboda ɗanˈuwanka ya dawo gida lafiya ƙalau.’

28 “Amma ɗanˈuwansa ya yi fushi sosai, ya ƙi yă shiga gida. Babansu kuwa ya fito ya ba shi haƙuri, ya roƙe shi yă shiga ciki.

29 Amma ya amsa wa babansa ya ce, ‘Duba, duk waɗannan shekaru, ina maka aiki kamar bawa, ban taɓa ƙin yin abin da ka ce in yi ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ˈyar akuya in kira abokaina mu ci da su ba!

30 Amma da ɗan nan naka ya dawo, wanda ya je ya cinye dukiyarka a kan karuwai, ka yanka masa saniyar nan mai ƙiba.’

31 Sai baban ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, duk abin da nake da shi, ai, naka ne.

32 Ya kamata mu yi murna da farin ciki, domin ɗanˈuwanka nan dā ya mutu, amma yanzu ya dawo, dā ya ɓace, amma yanzu an same shi.’ ”

Open Bible reader