Skip to content

Hausa Bible

Galatiyawa 1

1 Daga Bulus manzon Yesu. Ba daga wurin mutane ko ta wurin mutum ne kiran ya zo mini ba. Amma kiran ya zo mini ne daga Yesu Almasihu da Allah Uba wanda ya tā da shi daga matattu.

2 Dukan ˈyanˈuwan da suke tare da ni a nan su ma suna gai da dukan jamaˈar masu bi waɗanda suke a Galatiya.

3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu su kasance tare da ku.

4 Shi Yesu Almasihu ya ba da kansa domin zunubanmu, domin yă cece mu daga wannan mugun zamani. Wannan kuwa bisa ga nufin Allah Ubanmu ne.

5 Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.

6 Abin nan da kuke yi ya ba ni mamaki sosai. A cikin ɗan ƙanƙanin lokaci haka kuna so ku bar bin wanda ya kira ku ta wurin alherin Almasihu, har ma kuna komawa zuwa wani sabon labari dabam da labari mai daɗi namu.

7 Ai, babu wani labari mai daɗi dabam. Na faɗa haka ne domin akwai waɗansu da suke tā da hankalinku, suna kuma ƙoƙari su jujjuye gaskiyar labarin nan mai daɗi na Almasihu.

8 Amma ina gaya muku, idan waninmu zai kawo muku wani irin labari mai daɗi dabam da wanda muka kawo, ko shi malaˈika daga sama ne, ko mu da kanmu ma, to, bari yă zama laˈananne!

9 Kamar yadda muka riga muka faɗa muku a dā, ina sāke faɗa muku yanzu cewa duk wanda ya yi muku waˈazin wani irin labari mai daɗi dabam da wanda kuka riga kun karɓa, to, bari yă zama laˈananne!

10 Ko za a ce, ta wurin yin wannan magana haka ina ƙoƙari in sa mutane su yarda da ni ne? Aˈa. Abin da nake so shi ne, Allah yă yarda da abin da nake yi. Kuna tsammani ina ƙoƙari in faranta wa mutane rai ne? Aˈa. Da mutane ne nake faranta wa rai, da ban zama bawan Almasihu ba.

11 ˈYanˈuwana, ina so in faɗa muku cewa labari mai daɗin nan da nake yi muku waˈazinsa, ba daga wurin mutum ya fito ba.

12 Ban karɓe shi daga wurin mutum ba. Kuma ba wanda ya koya mini shi. Yesu Almasihu da kansa ne ya bayyana mini shi.

13 Kun ji irin zaman da dā na yi a cikin addinin Yahudawa, yadda na tsananta wa jamaˈar masu bin Allah ƙwarai da gaske, har na yi ta ƙoƙari in halaka ta.

14 Kun kuma san yadda a cikin addinin Yahudawa na fi yawancinsu waɗanda muka yi girma tare. Na fi su kishin bin alˈadun kakanninmu sosai.

15 Amma Allah wanda ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa ga alherinsa, har ya ji daɗi yă

16 bayyana mini Ɗansa Yesu, domin in yi waˈazin labari mai daɗi ga waɗanda ba Yahudawa ba. Da ya yi haka ban nemi shawara daga wajen wani mutum ba,

17 ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama manzanni ba. Abin da na yi shi ne, nan da nan na je ƙasar Arabiya, saˈan nan na komo Dimashƙu.

18 Sai bayan shekara uku ne na tafi Urushalima domin in ga Kefas wato, Siman Bitrus. Na kuwa yi kwana goma sha biyar tare da shi.

19 Bayan wannan kuma, ban ga ko ɗaya daga cikin sauran manzannin ba, sai dai Yakub ɗanˈuwan Ubangiji.

20 Abin nan da nake rubuta muku gaskiya ne a gaban Allah nake faɗa muku, ba ƙarya ba.

21 Daga baya kuma, na tafi ƙasar Suriya da ta Kilikiya.

22 Amma a wancan lokaci, jamaˈar masu bin Almasihu da suke cikin yankin Yahudiya, ba su san ni ido da ido ba tukuna.

23 Sun dai ji kawai an ce, “Mutumin nan wanda dā ya tsananta mana, ga shi yanzu yana sanar da maganar bangaskiyar nan da dā yake ɓatawa!”

24 Sai suka ɗaukaka Allah saboda abin da ya yi ta wurina.

Open Bible reader