Hausa Bible
Afisawa 5
1 Tun da yake kun zama ˈyaˈya waɗanda Allah yake ƙauna, sai ku ɗauki misali daga wurin Allah a cikin zamanku.
2 Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, baiko mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.
3 Kada ma a ko ambaci iskanci da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba.
4 Haka ma da ƙazamar magana da zancen banza da wawanci, gama ba su dace da ku ba. A maimakon haka ku dinga gode wa Allah.
5 Ku dai sani cewa, mai yin iskanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi, wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne, ba su da rabon gādo a mulkin Almasihu da Allah ko kaɗan.
6 Kada wani kuwa yă ruɗe ku da maganar wofi. Ai, saboda waɗannan zunubai ne fushin Allah yake zuwa a kan masu rashin biyayya.
7 Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
8 Domin dā kuna a duhu, amma a yanzu, kun sami haske ta wurin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske,
9 domin haske yake haifar da ayyuka masu kyau, da zaman adalci, da maganar gaskiya.
10 Ku tabbata cewa kun koyi abin da zai gamshi Ubangiji.
11 Ku rabu da ayyukan duhu marasa amfani, a maimakon haka ku tona su.
12 Gama abin kunya ne a ma faɗa abubuwan da suke yi a ɓoye.
13 Saˈad da aka kawo dukan abu a gaban haske, za a san ainihin yadda suke.
14 Shi ya sa aka ce, “Tashi, kai da kake barci! Ka tashi daga matattu! Almasihu kuwa zai haskaka ka.”
15 Saboda haka sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku. Kada ku zama kamar wawaye, sai dai kamar masu hikima.
16 Ku yi amfani da kowane zarafi na yin kirki, gama kwanakin da muke ciki yanzu mugaye ne.
17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.
18 Kada kuma ku bugu da ruwan inabi, wanda zai kai ku ga neman jin daɗi na rashin kunya. A maimakon haka ku cika da Ruhu,
19 ku yi magana da juna da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhaniya. Ku yi ta rera waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da dukan zukatanku.
20 Kullum ku dinga gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan dukan kome.
21 Ku miƙa kanku ga juna cikin tsoron Almasihu.
22 Ku matan aure, ku miƙa kanku ga mazanku, kamar yadda kuke yi wa Ubangiji.
23 Gama miji shi ne kan matarsa, kamar yadda Almasihu yake kan jamaˈar masu bi wato, jikinsa. Shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin.
24 Kamar yadda jamaˈar masu bi take miƙa kanta ga Almasihu, haka kuma mata su miƙa kansu ga mazansu ta kowane hali.
25 Ku maza ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci jamaˈar masu bi har ya ba da kansa dominta,
26 domin yă keɓe ta da tsarki ga Allah ta wurin maganarsa bayan da ya tsabtace ta ta wurin wanke ta da ruwa.
27 Ya yi wannan domin a saˈad da zai miƙa wa kansa jamaˈar masu bi, ta zama da daraja sosai ba tare da wani tabo ko wata alamar rashin kyan gani ba, ta kuma zama da tsarki, marar laifi kuma.
28 Ta haka ya kamata maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikinsu. Ai, wanda ya ƙaunaci matarsa, ya ƙaunaci kansa ke nan.
29 Domin ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi yă kula da shi sosai kamar yadda Almasihu yake kula da jamaˈar masu binsa.
30 Gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.
31 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Saboda haka mutum zai bar mamarsa da babansa, yă manne wa matarsa, su biyu su zama jiki ɗaya.”
32 Wannan asiri ne mai zurfi. Ni kuwa ina nufin Almasihu da jamaˈar masu bi ne.
33 Duk da haka dai, maganar ta shafe ku ku ma. Bari kowane ɗayanku yă ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta girmama mijinta.