Hausa Bible
Afisawa 1
1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga nufin Allah, zuwa ga tsarkaka waɗanda suke a Afisa, waɗanda suke da aminci cikin bin Almasihu Yesu.
2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu su kasance tare da ku.
3 Albarka ta tabbata ga Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu! Shi ne Allah wanda ta wurin Almasihu ya albarkace mu da kowace albarka ta ruhaniya cikin mulkinsa a sammai.
4 Ya zaɓe mu ta wurin zamanmu ɗaya da Almasihu tun ba a halicci duniya ba, domin mu zama masu tsarki, marasa laifi a gabansa. Saboda ƙaunarsa,
5 Allah ya riga ya ƙaddara mu mu zama ˈyaˈyansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri.
6 Ya yi haka domin mu yabi darajar alherinsa da ya ba mu kyauta a yalwace ta wurin Ɗansa da yake ƙauna.
7 Cikin Almasihu ne muka sami fansa ta wurin jininsa, wato yafewar zunubanmu, bisa ga alherinsa a yalwace,
8 wanda ya ba mu a yalwace da hikima marar iyaka da kuma basira.
9 Allah ya sa muka san asirin nufinsa bisa ga abin da ya nufa, wanda ya kuma shirya yă cika ta wurin Almasihu.
10 Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Almasihu, wato dukan abubuwan da suke a sama da abubuwan da suke a ƙasa gaba ɗaya.
11 A cikin Almasihu ne, aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga shirinsa, shi wanda yake aikata kome bisa ga nufinsa.
12 Ya zaɓe mu da nufi cewa mu da muka fara sa zuciya ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa.
13 Ta wurin Almasihu, ku ma kuka ji maganar gaskiya, wato labari mai daɗi na ceto. A saˈad da kuka ba da gaskiya ga Almasihu, Allah ya ba ku Ruhu Mai Tsarki kamar yadda aka yi muku alkawari zai yi, yă zama kamar hatimin shaida cewa ku nasa ne.
14 Ruhu Mai Tsarki shi ne tabbaci cewa Allah zai ba mu gādon da ya yi alkawari, wanda zai zama namu lokacin da Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.
15 Saboda haka da yake na ji labari yadda kuka ba da gaskiya ga Ubangiji Yesu, da kuma yadda kuke ƙaunar dukan tsarkaka,
16 ban fasa gode wa Allah saboda ku ba. Duk saˈad da nake yin adduˈa dominku, nakan yi haka
17 da nufi cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă dinga ba ku Ruhunsa mai ba da hikima da bayani domin ku ƙaru cikin sanin Allah.
18 Ina adduˈa kuma Allah yă sa haskensa a zuciyarku domin ku san ko mene ne sa zuciyar nan da ya kira ku a kanta, ku kuma san ko mene ne yalwar darajar albarkar gādon nan wanda yake domin tsarkaka.
19 Ina adduˈa har yanzu ku san ko mene ne girman ikonsa wanda ya wuce gaban misali, wanda yake aiki a cikinmu, mu da muka ba da gaskiya. Ikon nan da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan
20 wanda ya yi aiki cikin Almasihu saˈad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama mai daraja a hannun damansa a sama.
21 A can Almasihu yake mulki a kan dukan masu sarauta da iko da ƙarfi da mulki. Yana da suna wanda ya fi kowane suna da za a bayar, ba a duniyar nan kaɗai ba, har ma a zamani mai zuwa.
22 Allah kuma ya sa kome a ƙarƙashin ƙafafun Almasihu, ya kuma sa shi ya zama kai mai mulkin abu duka domin amfanin jamaˈar masu bi,.
23 wadda take jikin Almasihu. A cikin jamaˈar masu binsa kuma Almasihu cikakke ne, kamar yadda shi kansa ya ciccika dukan kome.