Hausa Bible
Matiyu 28
1 Ranar Hutu ta Mako ta wuce ke nan, a ranar farko ta mako da sassafe sai Maryamu daga Magadala da ɗayan Maryamu suka je su duba kabarin.
2 Ga shi kuwa an yi wata babbar rawar ƙasa, gama wani malaˈikan Ubangiji ya sauko daga sama, ya ture dutsen da aka rufe kabarin, ya zauna a kai.
3 Yana haske kamar walƙiya, rigunansa kuma farare fat kamar auduga.
4 Da masu gadin suka gan shi, tsoro ya kama su sosai, suna rawar jiki, suka fāɗi a ƙasa kamar matattu.
5 Amma malaˈikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, na sani kuna neman Yesu ne wanda aka gicciye.
6 Ba ya nan. Ya tashi yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda aka sa shi.
7 Ku je da sauri ku gaya wa almajiransa cewa, ‘Ya tashi daga matattu. Ga shi kuma zai riga ku zuwa Galili, a can ne za ku gan shi.’ Abin da na zo in gaya muku ke nan.”
8 Sai suka bar kabarin da sauri cike da tsoro, tare da farin ciki mai yawa. Suna gudu domin su je su faɗa wa almajiran Yesu ke nan,
9 sai Yesu da kansa ya sadu da su, ya ce musu, “Sallamarku dai!” Suka matso kusa suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada.
10 Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Ku je ku faɗa wa ˈyanˈuwana su tafi Galili, a can ne za su gan ni.”
11 Da matan suna cikin tafiya, sai waɗansu daga cikin masu gadin kabarin nan suka shiga gari, suka ba manyan firistoci labarin dukan abin da ya faru.
12 Sai firistocin da shugabannin mutane suka taru suka yi shawara, suka ba sojojin kuɗi mai yawa.
13 Suka ce, “Ku ce wa mutane, ‘Almajiransa ne suka je da dare suka sace shi lokacin da muke barci.’
14 Idan kuwa labarin ya kai kunnen gwamna, za mu yi masa magana, ba za ku shiga wahala ba.”
15 Sai sojojin suka karɓi kuɗin suka yi yadda aka ce su yi. Wannan labarin kuwa har wa yau Yahudawa suna ba da shi.
16 To, almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi Galili, suka je babban tudun da Yesu ya ce su sadu.
17 Da suka gan shi sai suka yi masa sujada, amma waɗansunsu suka yi shakka.
18 Sai Yesu ya zo kusa ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma nan duniya.
19 Saboda haka ku je ku faɗa wa dukan alˈumman duniya su bi ni, ku sa su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki.
20 Ku kuma koya musu su yi biyayya da dukan abubuwan da na umarce ku. Ga shi kuwa, ina tare da ku kullum har ƙarshen zamani.”