Hausa Bible
Matiyu 22
1 Sai Yesu ya sāke yi musu magana da misali ya ce,
2 “Za a iya kwatanta mulkin sama da wani sarkin da ya yi wa ɗansa bikin aure.
3 Ya aiki bayinsa su kira mutanen da aka gayyace su bikin, amma mutanen da aka gayyato ba su zo ba.
4 Ya sāke aiken waɗansu bayin ya ce, ‘Ku faɗa wa mutanen da aka gayyata cewa, “Ga shi na shirya abinci, an yanka shanu masu ƙiba da aka ciyar da su musamman. Duk an gama shirya kome. Ku zo bikin mana!” ’
5 Amma ba su kula ba. Suka tafi abinsu, wani ya tafi gonarsa, wani ya tafi kasuwancinsa,
6 waɗansu kuma suka kama bayin suka yi musu dūka, har suka kashe su.
7 Sarkin kuwa ya yi fushi sosai. Ya aika sojojinsa suka kakkashe masu kisan kan nan, har suka ƙone garinsu tas.
8 Saˈan nan ya ce wa bayinsa, ‘An gama shirin bikin, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba.
9 Saboda haka ku bi titi-titi ku ce wa duk waɗanda kuka samu su zo bikin.’
10 Bayin nan kuwa suka bi titi-titi suka tattaro duk waɗanda suka samu, na kirki da waɗanda ba na kirki ba, har wurin bikin ya cika da baƙi.
11 “Amma da sarkin ya shigo domin yă ga baƙin, sai ya ga wani mutum bai sa rigar biki ba.
12 Sai ya ce wa mutumin, ‘Aboki, yaya aka yi ka shigo nan ba tare da ka sa rigar biki ba?’ Amma mutumin ya rasa abin da zai faɗa.
13 Sai sarkin ya ce wa masu yi masa hidima, ‘Ku ɗaure hannuwansa da ƙafafunsa, ku jefa shi cikin mugun duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’
14 “Ai, an kira mutane da yawa, amma kaɗan ne aka zaɓa.”
15 Ana nan sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su yi masa tarko cikin abin da zai faɗa.
16 Sai suka aiko da almajiransu tare da waɗansu mutanen Hirudus suka ce, “Malam, mun sani kai mai gaskiya ne, kana kuma koyar da hanyar Allah cikin gaskiya, domin mutane duk ɗaya ne a gare ka, gama ba ka nuna bambanci tsakanin mutane.
17 To, ka gaya mana, kana gani daidai ne mu biya wa Kaisar babban sarkin Roma haraji, ko aˈa?”
18 Amma saboda Yesu ya gane ƙiyayyar zuciyarsu sai ya ce, “Don me kuke gwada ni, ku munafukai?
19 Ku nuna mini kuɗin da ake biyan harajin da shi.” Sai suka kawo masa dinari.
20 Sai ya ce musu, “Hoton nan da sunan nan na wane ne?”
21 Suka amsa suka ce, “Na Kaisar ne.” Sai Yesu ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”
22 Da suka ji haka, sai suka kama baki suna mamaki, suka bar shi, suka tafi.
23 A ranar nan kuwa, waɗansu Sadukiyawa suka zo wurin Yesu. Su ne suke cewa wai babu tashin matattu. Suka tambaye shi,
24 suka ce, “Malam, Musa ya ce, ‘Idan mutum ya mutu ba shi da ɗa, sai ɗanˈuwansa yă auri matar domin yă haifa wa ɗanˈuwansa ˈyaˈya.’
25 To, akwai waɗansu ˈyanˈuwa guda bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai haifu ba, ya bar wa ɗanˈuwansa matarsa.
26 Haka ya faru da na biyun, da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin.
27 Daga ƙarshe, sai matar ta mutu.
28 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Gama dukansu sun aure ta.”
29 Yesu ya amsa musu ya ce, “Tunaninku ba daidai ba ne, gama ba ku san Rubutacciyar Maganar Allah ba, kuma ba ku san ikon Allah ba.
30 Ai, a tashin matattu, maza ba za su yi aure ba, mata kuma ba za a ba da su ga aure ba, sai dai za su zama kamar malaˈikun Allah.
31 Kuma game da tashin matattu, ba ku karanta abin da Allah ya faɗa muku ba? An rubuta cewa,
32 ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yakub.’ Shi Allah na masu rai ne, ba na matattu ba.”
33 Da mutane suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
34 Da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, sai suka taru.
35 Wani malamin Koyarwar Musa a cikinsu ya yi wa Yesu tambaya domin yă gwada shi.
36 Ya ce, “Malam, wace doka ce ta fi girma a cikin dokoki?”
37 Yesu ya amsa masa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka.’
38 Wannan ita ce doka ta farko, kuma mafi girma.
39 Ta biyun ma kamar ta farkon take, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka.’
40 Dukan Koyarwar Musa da ta annabawa sun rataya a kan waɗannan dokoki biyu.”
41 Da Farisiyawa suka taru wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su
42 ya ce, “Mene ne tunaninku game da Almasihu? Ɗan wane ne shi?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”
43 Sai Yesu ya ce musu, “To, yaya Dawuda ta ikon Ruhu yake ce da shi ‘Ubangiji’? Gama Dawuda ya ce,
44 “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna nan a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin ƙafafunka.” ’
45 “Idan Dawuda yana ce da Almasihu ‘Ubangiji’, to, yaya Almasihu ya zama ɗansa?”
46 Ba wanda ya iya ba shi amsa. Daga ranar nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin yă sāke yi masa tambaya.