Skip to content

Hausa Bible

Afisawa 6

1 Ku ˈyaˈya, saboda Ubangiji ku yi wa iyayenku biyayya, domin wannan shi ne daidai.

2 Doka ta fari wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Girmama babanka da mamarka,

3 domin ka sami zaman lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”

4 Ku ubanni, kada ku sa ˈyaˈyanku su yi fushi, sai dai ku goye su da horo da gargaɗi ta hanyar Ubangiji.

5 Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniyar nan. Ku nuna musu halin ban girma, kuna yi musu aminci cikin dukan kome, da zuciya ɗaya kuma, kamar yadda kuke yi wa Almasihu.

6 Kada ku yi biyayya ta ganin ido, kamar waɗanda suke neman yabo daga wurin mutane, amma da yake ku bayin Almasihu ne, ku aikata abin da Allah yake so da zuciya ɗaya.

7 Ku yi aikinku na hidima da kyakkyawan nufi, kamar ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba.

8 Kun sani cewa kowane alherin da mutum ya yi, ko shi bawa ne ko ɗan gida ne, Ubangiji zai ba shi ladansa.

9 Ku iyayengiji, ku ma ku yi wa bayinku haka. Ku daina ba su tsoro, tun da yake kun sani ku da su duk kuna da Ubangiji a sama, shi kuwa ba ya nuna bambanci.

10 A ƙarshe kuma ku ƙarfafa kanku cikin Ubangiji da kuma cikin ƙarfin ikonsa.

11 Ku ɗaura wa jikinku dukan kayan kāriya yaƙi wanda Allah ya bayar domin ku iya tsayawa ku yi gāba da dabarun Shaiɗan.

12 Ai, ba da ˈyan Adam masu nama da jini muke kokawa ba, amma da mugayen ruhohi ne na sammai, da masu mulki, da ikoki, da waɗanda mulkin zamanin nan mai duhu yake hannunsu.

13 Saboda haka sai ku ɗauki dukan kayan kāriya na yaƙi wanda Allah ya bayar domin ku tsaya a muguwar ranar nan, har bayan da kuka gama kome da kome, a same ku a tsaye.

14 Saboda haka fa ku tsaya da ƙarfi, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci yă zama rigar ƙarfenku ta yaƙi.

15 Shirin kai labari mai daɗi na salama, yă zama kamar takalma a ƙafafunku.

16 Ban da haka ma, bari bangaskiya ta zama garkuwarku wadda za ku ɗauka ku kashe kibiyoyi na wutar Mugun nan da ita.

17 Ku ɗauki hular kwano, wato ceto, da kuma takobin Ruhu, wato Kalmar Allah.

18 Kuna yin adduˈa kullum ta wurin ikon Ruhu, kuna yin roƙo iri-iri. Da nufi haka, ku yi tsaro da iyakar naciya yayin da kuke adduˈa saboda tsarkaka.

19 Ni ma ku yi mini adduˈa, in sami baiwar yin magana ba tsoro, in sanar da asirin labari mai daɗi ga mutane.

20 Ta dalilin wannan labari mai daɗi ne na zama wakili, ko da yake ina ɗaure! Ku yi mini adduˈa domin duk lokacin da nake yin waˈazi in yi shi ba tsoro kamar yadda ya kamata in yi.

21 Tikikus, ɗanˈuwanmu wanda muke ƙauna, mai hidima cikin aminci kuma ga Ubangiji, zai sanar da ku kome domin ku ma ku san yadda nake da lafiya da kuma halin da nake ciki.

22 Na aike shi gare ku musamman domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.

23 ˈYanˈuwa, salama daga Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu ta kasance a cikinku, tare da ƙauna da bangaskiya.

24 Alheri yă kasance tare da dukan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙārewa. Amin.

Open Bible reader