Hausa Bible
Zabura 99
1 Ubangiji Sarki ne, Mutane suna rawar jiki, Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi, Duniya ta girgiza.
2 Ubangiji mai iko ne a Sihiyona, Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma.
3 Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki, Mai Tsarki ne shi!
4 Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai, Ka kawo adalci cikin Isra'ila, Ka kawo adalci da gaskiya.
5 Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a gaban kursiyinsa! Mai Tsarki ne shi!
6 Musa da Haruna firistocinsa ne, Sama'ila kuma mai yi masa sujada ne. Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu.
7 Ya yi magana da su daga girgije, Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su.
8 Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama'arka, Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara, Amma kakan hukunta su saboda zunubansu.
9 Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki! Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne!