Hausa Bible
Zabura 87
1 Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai,
2 Yana ƙaunar birnin Urushalima fiye da kowane wuri a Isra'ila.
3 Ya birnin Allah, ka kasa kunne, Ga abubuwan banmamaki da ya faɗa a kanka.
4 “Sa'ad da na lasafta sauran al'umma da suke yi mini biyayya, Zan sa Masar da Babila a cikinsu, Zan ce da Filistiya, da Taya, da Habasha, Su ma na Urushalima ne.”
5 A kan Sihiyona kuwa za a ce, “Dukan sauran al'umma nata ne.” Maɗaukaki kuwa zai ƙarfafa ta.
6 Ubangiji zai rubuta lissafin jama'o'i, Ya sa su duka cikin jimilla ta Urushalima.
7 Duk mazauna a wurin za su raira waƙa, su yi rawa, Su ce, “Dukan maɓuɓɓugaina suna cikinka.”