Hausa Bible
Zabura 82
1 Allah yana matsayinsa a taron jama'arsa, Yakan zartar da nufinsa a taron alloli.
2 Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a, Ku daina goyon bayan mugaye!
3 Ku kāre hakkin talakawa da na marayu, Ku yi adalci ga matalauta, Da waɗanda ba su da mataimaki.
4 Ku kuɓutar da talakawa da matalauta, Ku cece su daga ikon mugaye!
5 “Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye! Kuna zaune cikin duhu, Ga shi, ba adalci a duniya sam!
6 Na faɗa muku, ku alloli ne, Cewa dukanku 'ya'ya ne na Maɗaukaki.
7 Amma za ku mutu kamar kowane mutum, Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”
8 Ya Allah, ka zo, ka mallaki duniya, Dukan al'ummai naka ne.