Skip to content

Hausa Bible

Zabura 75

1 Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka! Muna shelar sunanka mai girma, Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata!

2 “Na ƙayyade lokacin yin shari'a,” in ji Ubangiji Allah, “Zan kuwa yi shari'ar gaskiya.

3 Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace, Zan ƙarfafa harsashin gininta.

4 Na faɗa wa masu girmankai kada su yi taƙama, Na kuma faɗa wa mugaye kada su yi fāriya,

5 Na dai faɗa musu su daina yanga, Su daina yin taƙama.”

6 Hukunci ba daga gabas, ko yamma, Ko daga kudu, ko arewa yake zuwa ba.

7 Allah yake yin shari'a, Yana ƙasƙantar da waɗansu, ya kuma ɗaukaka waɗansu.

8 Ubangiji yana riƙe da ƙoƙo, Cike da sabon ruwan inabi mai ƙarfi, Yana zuba shi, dukan mugaye kuwa suna ta sha, Suka shanye shi ƙaƙaf.

9 Amma har abada ba zan daina yin magana a kan Allah na Yakubu ba, Ko in daina raira yabbai gare shi.

10 Shi zai karya ikon mugaye, Amma za a ƙara wa masu adalci ƙarfi.

Open Bible reader