Hausa Bible
Zabura 64
1 Ina shan wahala, ya Allah, ka ji addu'ata! Ina jin tsoro, ka cece ni daga maƙiyana!
2 Ka kiyaye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, Da iskancin mugayen mutane.
3 Sukan wasa harsunansu kamar takuba, Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.
4 Sukan yi kwanto su harbi mutanen kirki da kibau, Nan da nan sukan yi harbi, ba su kuwa jin tsoro.
5 Suna ƙarfafa junansu cikin yin mugayen ƙulle-ƙullensu, Sukan yi ta taɗi a kan inda za su kafa tarkunansu. “Ba wanda zai gan mu,” in ji su.
6 Sukan shirya maƙarƙashiya, su ce, “Ai, mun gama shirin aikata laifi sarai.” Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa!
7 Amma Allah zai harbe su da kibansa, Za a yi musu rauni nan da nan.
8 Zai hallaka su saboda maganganunsu, Duk wanda ya gan su zai kaɗa kansa.
9 Dukansu za su ji tsoro, Za su faɗi abin da Allah ya aikata, Su yi tunani a kan ayyukansa.
10 Dukan masu adalci za su yi murna, Saboda abin da Ubangiji ya aikata. Za su sami mafaka a gare shi, Dukan mutanen kirki za su yabe shi.