Skip to content

Hausa Bible

Zabura 54

1 Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah, Ka cece ni ta wurin ƙarfinka!

2 Ka ji addu'ata, ya Allah, Ka saurari kalmomina!

3 Masu girmankai sun tasar mini, Mugaye suna nema su kashe ni, Mutanen da ba su kula da Allah ba.

4 Na sani Allah ne mai taimakona, Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona!

5 Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu! Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne.

6 Da murna zan miƙa maka hadaya, Zan yi maka godiya, ya Ubangiji, Domin kai mai alheri ne.

7 Ka cece ni daga dukan wahalaina, Na kuwa ga an kori maƙiyana.

Open Bible reader