Skip to content

Hausa Bible

Zabura 47

1 Ku yi tāfi saboda farin ciki, Ya ku jama'a duka! Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah!

2 A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka, Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.

3 Ya ba mu nasara a bisa jama'o'i, Ya sa muka yi mulkin al'ummai,

4 Ya zaɓar mana ƙasar da muke zaune, Wadda take mallaka ce ta fāriya, ta jama'arsa Wadda yake ƙauna.

5 Allah ya hau kan kursiyinsa! Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni, Lokacin da Ubangiji yake hawa!

6 Ku raira yabbai ga Allah, Ku raira yabbai ga sarkinmu!

7 Allah sarki ne na duniya duka, Ku yabe shi da waƙoƙi!

8 Allah yana zaune kan kursiyinsa mai tsarki, Yana mulkin al'ummai,

9 Masu mulkin al'ummai suka tattaru Tare da jama'ar Allah na Ibrahim. Allah shi ne garkuwar jarumawa, Yana mulkin duka!

Open Bible reader