Hausa Bible
Zabura 3
1 Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji, Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni!
2 Suna magana a kaina, suna cewa, “Allah ba zai taimake shi ba!”
3 Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari, Kana ba ni nasara, Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.
4 Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako, Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsensa.
5 Na kwanta na yi barci, Na kuwa tashi lafiya lau, Gama Ubangiji yana kiyaye ni.
6 Ba na jin tsoron dubban abokan gāba Waɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.
7 Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana, Ka hallakar da dukan mugaye.
8 Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji, Bari yă sa wa jama'arsa albarka!