Hausa Bible
Zabura 26
1 Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji, Gama na yi abin da suke daidai, Na dogara gare ka gaba ɗaya.
2 Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji, Ka gwada muradina da tunanina.
3 Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni, Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin.
4 Ba na tarayya da mutanen banza, Ba abin da ya gama ni da masu riya.
5 Ina ƙin tarayya da masu mugunta, Nakan kauce wa mugaye.
6 Ya Ubangiji, na wanke hannuwana Don in nuna ba ni da laifi, Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.
7 Na raira waƙar godiya, Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.
8 Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake, Inda ɗaukakarka yake zaune.
9 Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi, Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,
10 Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci, A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.
11 Amma ni, ina yin abin da yake daidai, Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!
12 Na kuɓuta daga dukan hatsarori, A taron sujada na yabi Ubangiji!