Skip to content

Hausa Bible

Zabura 149

1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji Ku yabe shi cikin taron jama'arsa masu aminci!

2 Ki yi murna, ke Isra'ila, sabili da Mahaliccinki, Ku yi farin ciki, ku jama'ar Sihiyona, sabili da Sarkinku!

3 Ku yabi sunansa, kuna taka rawa, Ku kaɗa bandiri da garayu, kuna yabonsa.

4 Ubangiji yana jin daɗin jama'arsa, Yakan girmama mai tawali'u ya sa ya ci nasara.

5 Bari jama'ar Allah su yi farin ciki saboda cin nasararsu, Su raira waƙa don farin ciki.

6 Bari su yi sowa da ƙarfi Sa'ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi.

7 Don su ci nasara bisa al'ummai, Su kuma hukunta wa jama'a,

8 Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi, Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe,

9 Su hukunta wa al'ummai, kamar yadda Allah ya umarta. Wannan shi ne cin nasarar jama'ar Allah! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Open Bible reader