Hausa Bible
Zabura 131
1 'Ya Ubangiji, na rabu da girmankai, Na bar yin fariya, Ba ruwana da manyan al'amura, Ba ruwana kuma da zantuttukan da suka fi ƙarfina.
2 Amma na haƙura, raina a kwance, Kamar jinjirin da yake kwance jalisan a hannun mahaifiyarsa, Haka zuciyata take kwance.
3 Ya Isra'ila, ka dogara ga Ubangiji, Daga yanzu har abada!