Hausa Bible
Zabura 130
1 A cikin fid da zuciyata, Na yi kira gare ka, ya Ubangiji.
2 Ka ji kukana, ya Ubangiji, Ka kasa kunne ga kiran da nake yi na neman taimako!
3 Idan kana yin lissafin zunubanmu, Wa zai kuɓuta daga hukunci?
4 Amma kakan gafarta mana, Domin mu zama masu tsoronka.
5 Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji, Ga maganarsa na dogara.
6 Ina jiran Ubangiji, Na zaƙu ƙwarai, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir, I, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir.
7 Ya Isra'ila, ki dogara ga Ubangiji, Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce, A koyaushe yana da nufin yin gafara.
8 Zai fanshi jama'arsa Isra'ila Daga dukan zunubansu.