Skip to content

Hausa Bible

Zabura 126

1 Sa'ad da Ubangiji ya komar da mu cikin Sihiyona, Sai abin ya zama kamar mafarki!

2 Muka kece da dariya, muka raira waƙa don farin ciki, Sa'an nan sai sauran al'umma suka ambace mu, suka ce, “Ubangiji ya yi manyan al'amura masu girma, sabili da su!”

3 Hakika ya aikata manyan al'amura sabili da mu, Mun kuwa yi farin ciki ƙwarai!

4 Ya Ubangiji, ka komar da mu ƙasarmu Kamar yadda ruwan da kake yi yakan koma cikin busassun koguna,

5 Ka sa waɗanda suke kuka a lokacin da suke dashe, Su tattara albarkar kaka da farin ciki!

6 Su waɗanda suka yi kuka a sa'ad da suka fita suna ɗauke da iri, Za su komo ɗauke da albarkar kaka, Suna raira waƙa don farin ciki!

Open Bible reader