Skip to content

Hausa Bible

Zabura 124

1 Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu, Da me zai faru? Ba da amsa, ya Isra'ila!

2 “Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu, A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana,

3 Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan, Saboda zafin fushi da suke yi da mu,

4 Da rigyawa ta kwashe mu, Da ruwa yi ci mu,

5 Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.”

6 Sai mu gode wa Ubangiji, Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba.

7 Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta, Tarkon ya tsinke, mun 'yantu!

8 Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa, Shi wanda ya yi sama da duniya.

Open Bible reader