Hausa Bible
Zabura 122
1 Na yi murna sa'ad da suka ce mini, “Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!”
2 Ga shi kuwa, mun iso, Muna tsaye a ƙofofin Urushalima!
3 Urushalima birni ce wadda aka maido ta yadda take dā, Da kyakkyawan tsari, a shirye!
4 A nan kabilai sukan zo, Kabilan Isra'ila, Domin su yi godiya ga Ubangiji, Kamar yadda ya umarce su.
5 A nan majalisu suke, Wurin da sarki yake yi wa jama'arsa shari'a.
6 Ku yi wa Urushalima addu'ar salama! “Allah ya sa masu ƙaunarki su arzuta!
7 Salama ta samu a garukanki, Da zaman lafiya kuma a fādodinki.”
8 Saboda abokaina da aminaina, Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!”
9 Saboda Haikalin Ubangiji, Allahnmu, Ina addu'a domin ki arzuta.