Hausa Bible
Zabura 121
1 Na duba wajen duwatsu, Daga ina taimakona zai zo?
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.
3 Ba zai bar ka ka fāɗi ba, Makiyayinka, ba zai yi barci ba!
4 Makiyayin Isra'ila, Ba ya gyangyaɗi ko barci!
5 Ubangiji zai lura da kai, Yana kusa da kai domin ya kiyaye ka.
6 Ba za ka sha rana ba, Ko farin wata da dare.
7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari, Zai sa ka zauna lafiya.
8 Zai kiyaye shigarka da fitarka, Tun daga yanzu har abada.