Hausa Bible
Zabura 110
1 Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina, “Zauna nan a damana, Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”
2 Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce, “Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”
3 A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu. Kamar yadda raɓa take da sassafe, Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.
4 Ubangiji ya yi muhimmin alkawari, Ba kuwa zai fasa ba! “Za ka zama firist har abada Bisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”
5 Ubangiji yana damanka, Zai kori sarakuna a ranar da ya husata.
6 Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma, Ya rufe fagen fama da gawawwaki, Zai kori sarakunan duk duniya.
7 Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya, Ya wartsake ya sami ƙarfi. Zai yi tsayawar nasara.