Hausa Bible
Zabura 11
1 Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya, Wauta ce idan kun ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu,
2 Domin mugaye sun ja bakkunansu, Sun kuma ɗana kibansu Domin su harbi mutanen kirki a duhu.
3 Ba abin da mutumin kirki zai iya yi Sa'ad da kome ya lalace.”
4 Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa, Yana da kursiyinsa a Sama. Yana kallon dukan mutane Yana sane da abin da suke yi.
5 Yana auna masu kirki da mugaye dukka, Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.
6 Yakan aukar da garwashin wuta Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye, Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.
7 Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar kyawawan ayyuka, Masu yi masa biyayya za su zauna a gabansa.