Hausa Bible
Zabura 100
1 Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!
2 Ku yi wa Ubangiji sujada da murna, Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!
3 Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah! Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne, Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.
4 Ku shiga Haikalinsa da godiya, Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi! Ku gode masa, ku yabe shi!
5 Ubangiji nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce, Amincinsa kuwa har abada abadin ne.